Babbaka mutum da wuta gayar azaba ce

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ko a lahira babbar azaba ga mujurmai da wuta za a yi. Ita kuwa wutar lahira makamashin ta mutane ne da su ka saɓa wa Allah da duwatsu kamar yadda ya zo a aya ta 6 ta Suratul Tahrim.

A nan duniya ma ai ba azabar da ta wuce a ƙona mutum ko a babbaka shi da ransa a wuta. Son samu aikin wuta irin wannan ta makamashi a girka abinci da ita a sha, amma in ta zama girka mutum ake yi a cikinta, to an gama mummunan mataki. Kai yau ko hukuncin kisa ake yanke wa mutum ba a jefa shi a wuta ya mutu ta wannan hanyar.

Yaya ma mutum ya ke ji in ya taka garwashi ko a ya taɓa sanwa mai zafi ko ya kurɓa kunu mai zafi?. Gaskiya ba daɗi sam. Na san da yardar Allah masu karatu sun fahimci inda na dosa wato yankin Sabon Birni na jihar Sokoto inda miyagun iri suka ƙure iya muguntarsu. Wannan mugunta ita ce ta buɗe wuta kan motar safa da ‘yan bindiga suka yi bayan nan su ka ƙona mutum 42 ƙurmus. Cikin waɗanda a ka ƙona har da jariri ko jaririya da ke cikin mahaifiya. Yankin Arewa-maso-yamma ya zama yanki mai hatsarin shiga musamman jihar Sokoto, Katsina da Zamfara.

Haka nan ma sananniyar hanyar Abuja zuwa Kaduna da jihar Neja a Arewa ta tsakiyar Nijeriya. Abin kamar wani haɗin baki don daga 2009 yankin Arewa-maso-gabas ke fama da ‘yan ta’addan Boko Haram da kan kama garurruwa da sunan kafa daula inda su kan yanke wa mutane huncin kisa ta hanyar bindige su ko yanka su kamar rago.

Ba zan tuna ganin inda su ka tare mota su ka banka wa mutane wuta ba duk da su ma ta’ddancin na su ya kai ƙololuwa. Yanzu kuma lamarin ya juya Arewa-maso-yamma inda yadda a baya ake ganin jerin gawarwaki a Arewa-maso-gabas ana musu salla, yanzu kuma a Arewa-maso-yamma ake ganin jerin gawarwakin. Arewa ta tsakiya ma sammakal don in an duba abun da ya faru a Filato da Binuwai. Da wannan bayani dai za mu lura kusan dukkan arewa na cikin babbar jarrabawa da jami’an tsaro ko gwamnatoci kaɗai ba za su iya magance matsalar ba.

Hakan ya nuna sai kowa ya yi nazari ya duba hagu da daman sa don sanin tudun mun tsira. Ga farar hula ko talakawa ya na da kyau su zama tsuntsiya maɗaurin ta ɗaya ta hanyar aiki tare dare da rana da kula da gewayen su. Kazalika a duƙufa ga addu’a bayan gyara ɗabi’u ta hanyar kaucewa zalunci, ha’inci da lalaci. Wani abin damuwa shi ne yadda rikicin ‘yan bindigar ke neman rikiɗewa na ƙabilanci tsakanin Fulani da Hausawa ko yadda ɗaya daga ‘yan bindigar ya shirya maulidi da ɗaukar matakan rufe masallatan waɗanda ba su halarci maulidin ba a ƙaramar hukumar Shinkafi.

Haƙiƙa sai an yi takatsantsan don in ƙalubalen ya ƙara ƙarfi ta ƙabilanci ga wani na neman shigo da addini to akwai babbar damuwa na wata guguwar da sai dai mu ce Allah ya kiyaye. Tuni dai wasu manya da matasa na Arewa sun shiga bayyana ra’ayoyinsu.

Tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa ya nuna rashin daɗi ga rashin ziyartar Sokoto da shugaba Buhari ya yi biyo bayan buɗe wuta kan motar safa da ƙona fasinjoji da ‘yan bindiga suka yi. Bafarawa ya ce, maimakon shugaban ya tafi Sokoto don jajantawa sai ya tafi Legas ƙaddamar da littafin tarihin ɗan siyasa Bisi Akande.

Tsohon gwamnan wanda kan fito lokaci-lokaci yana magana kan lamuran ƙasa musamman yankin Arewa, ya ce, shugaba Buhari kamar ba ya kulawa ga rayuwar al’ummar Zamfara, Sokoto da Katsina da ke fama da illar ‘yan bindiga.

Duk da haka Bafarwa a fuskar adalcin magana ya ce, shugaba Buhari ya tura tawaga ta wakilce shi a jajantawar; ya na mai nuna duk da haka da ya zo da kan sa kamar yadda ya yi a lokacin yakin neman zaɓe.

A matsayinsa na tsohon gwamnan Sokoto na shekaru 8, Bafarawa ya ce, ya san abin da a ke nufi da in an rantsar da mutum da Alkur’ani ko da Baibul, ya zama wajibi a kan sa ya tsaya ga kare rayuka da dukiyar jama’a.

Tuni wasu ‘yan arewa akasari bisa jagorancin mata suka ƙaddamar da wata zanga-zanga a Abuja don jan hankalin gwamnati ta ɗauki matakan dakatar da kashe-kashen da ‘yan bindiga ke yi musamman a Arewa-maso-yamma.

Duk da dai jami’an tsaro sun killace ‘yan zanga-zanga a iya dandalin ‘UNITY FOUNTAIN’ wasu ƙarin mutane sun bayyana ƙudurin gudanar da ƙarin zanga-zangar.

Ba mamaki tura tawaga da shugaba Buhari ya yi ƙarƙashin mai ba shi shawara kan tsaro Manjo Janar Babagana Monguno zuwa Arewa-maso-yamma; amsa irin ƙorafin ƙungiyoyi ne ciki da Jama’atu Nasril Islam da ke son matakai na zahiri don dakatar da zubar da jinin jama’a haka siddan.

Da alamun ‘yan zanga-zangar ba su yi la’akari da yadda ‘yan dawo-da-matan Chibok BBOG ba su kwashe nika da waƙa ba bayan tarwatsa su da aka yi, sun yi alwashin tsayin daka sai sun bi ta titin nan na Shehu Shagari da ke daura da majalisar dokoki, kotun ƙoli, fadar Aso Rock da helkwatar ‘yan sanda.

Ɗaya daga jagororin zanga-zangar Zainab Ahmad ta yi tambayoyi ko miqa buƙatu ga gwamnati kan tsaron da ta ke ganin in haka ta tadda ruwa za a samu sararawa.

A daidai lokacin da a ke wannan batu na tsaro, wata ƙungiyar cigaban Funtua ƙarƙashin limamin masallacin ZONE B na gidajen ‘yan majalisar tarayya Ibrahim Auwal Usama, ta ce, za ta shigar da shugaba Buhari ƙara matuƙar ba a janye shirin ƙarin farashin fetur ba zuwa nan da mako uku. Ƙungiyar na ganin ƙara farashin man fetur zai ƙara ta’azzara lamuran rashin tsaro ne. Don da alamun ɗaya daga manyan dalilan taɓarɓarewar tsaro akwai ƙuncin rayuwa da tsadar farashin kayan masarufi ke yi. Ba baƙon abu ba ne idan an ƙara farashin fetur, farashin kayan masarufi kan tashi.

Haka rayuwa ta ke wasu na kuka wasu na dariya a ƙasashen da akasarin mutane ba su tsallake mizanin talauci na Majalisar Ɗinkin Duniya na samun dala ɗaya a wuni ba, wato yanzu wajen Naira 560 a kasuwar canji.

Ba ma jayayya da masu zanga-zanga kan taɓarɓarewar tsaro – Fadar shugaban ƙasa

Fadar gwamanatin Nijeriya ‘Aso Rock’ ta ce, ba ta jayayya da masu zanga-zanga kan taɓarɓarewar tsaro ta hanyar buƙatar ɗaukar matakin da ya dace.

Aso Rock na magana kan zanga-zanga da wasu ‘yan Arewa su ke yi a Abuja da Kano don jan hankalin gwamnati ta ɗauki matakan dakatar da zubar da jinin jama’a musamman biyo bayan ƙona mutane da ran su a motar safa a yankin Sabon Birni na jihar Sokoto.

Mai taimaka wa shugaba Buhari kan labaru Garba Shehu ya ce, ba laifi ba ne mutane su yi magana kan abin takaicin da ke faruwa wanda gwamnatin tuni ta tura manyan jami’an tsaro na sirri zuwa yankunan da lamarin ya ta’azzara don jajantawa da ɗaukar matakan da su ka dace na magance miyagun iri.

Garba Shehu ya ce, abin da ke kan teburin shugaba Buhari shi ne matakin kare rayuka da dukiyoyin al’umma; da hakan ke buƙatar goyon bayan dukkan jama’a.

Jami’in labarun fadar gwamnatin ya ce, ai an samu lokacin da wasu ke zuba kuɗin tsaron a aljihun su ba a jin ɗuriyar komai “bai dace a sanya siyasa a lamarin tsaro ba, ƙalubale ne da ya shafi dukkan ‘yan Nijeriya ba bambancin siyasa.”

Shehu ya ce, jami’an sirrin ƙarƙashin mshawarcin shugaban ƙasa kan harkokin tsaron ƙasa, Manjo Janar Baba Gana Monguno (mai ritaya) sun tattauna da jama’ar yankunan da illar ta yi tsanani kuma za a yi amfani da bayanan sirri wajen murƙushe masu kisan gilla.

Daidai lokacin da a ke wannan juyayi sai a ka samu labarin kisan gilla ga kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina Dr.Rabe Nasir a gidan sa da ke Katsina. Marigayin wanda masanin tsaro ne, ya sha ba da gudunmawa ga magance ƙalubalen tsaro a Arewa, amma cikin ƙaddarawar da Allah ya yi ma sa, ƙalubalen ne ya yi sanadiyyar rasa ransa!

Ko yaya za a ɗauki wannan lamari ya wuce barazanar kan manyan hanyoyi ko ƙungurmin daji da ƙauyuka, miyagun iri kan iya tarar da mutum har ɗakin kwanansa su hallaka shi. Shi ya sa mutane yanzu zai yi wuya su riƙa barci da minshari da zarar mutum ya ji saraf sai ya yi farat.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *