Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jagoran adawa na Nijeriya, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Nijeriya da sakacin da ya kai ga kisan Sarkin Gobir na Gatawa, Alh. Isa Bawa.
A ranar Laraba ne dai aka samu labarin mutuwar sarkin wanda ‘yan bindigar da ke garkuwa da shi suka kashe, bayan kasa kai musu kuɗin fansar da suka buƙata domin sakin sarkin tare da ɗansa, kamar yadda makusantansa suka shaida.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na ɗ, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar PDP ya ce sakacin gwamnati da na jami’an tsaro ne suka janyo mutuwar sarki.
”Halin ko’in kula da gwamnati ta nuna, da rashin ingantaccen tsari daga jami’an tsaro sun taimaka wajen yaɗuwar irin waɗannan abubuwa na sosa zuciya a lokutan baya-bayan nan,” inji Atiku Abubakar.
”Yana da muhimmanci mu ƙara jaddada wa gwamnati cewa dole ne ta samar da tsaron rayukan jama’a ta yadda mutane ba za su rayu cikin fargabar fusknatar irin haka ba,” in ji tsohon mataimakin shugaban ƙasar.
Atiku Abubakar ya nuna alhininsa kan rasuwar sarkin tare da miƙa saƙon ta’aziyyarsa ka iyalai da ɗaukacin al’ummar masarautar Gobir, da gwamnatin jihar Sakkwato kan mutuwar sarkin da ya bayyana a matsayin mai ”cike da tashin hankali”.
