A cikin awa takwas, attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon Musk, ya sami Dalar Amurka biliyan 14, wato Naira tiriliyan shida, kwatankwacin ilahirin abin da wanda ya fi kowa kuɗi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya mallaka.
Kuɗin dai, waɗanda ya samu ranar Larabar makon da ya gabata, sun haura Dala biliyan 13.9 da Dangote ya mallaka, wanda shi ne na 65 a jerin attajiran duniya.
Tattalin arzikin Dangote ya ragu a ranar Talata, bayan ya tafka asarar Naira biliyan 105.33, lamarin da ya sa kuɗin nasa suka ragu da kashi -1.78.
A cewar jaridar Bloomberg, kaso 86 cikin 100 na kuɗin Dangote na cikin kamfanin simintinsa na Dangote Cement, wanda ya sami kuɗin shigar Naira tiriliyan 1.38 a shekarar 2021.
Sai dai duk da haka yana harkar sukari da gishiri da mai da takin zamani da kuma abinci.
Kazalika, Dangote na ɗaya daga cikin masu hannun jari a bankin UBA.