02
Nov
Daga BELLO A. BABAJI Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi alla-wadai da tsare ƙananan yara 67 da ƴan sanda suka yi a Abuja kan zargin su da shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a watan Agusta. Kwankwaso ya nuna damuwa matuƙa kan yadda aka bar su babu kulawa sakamakon rashin ba su isasshen abinci, ya na mai kira da a gaggauta ba su kulawa ta lafiya. Ya ce, hakan ya saɓa wa ƴancinsu na ƴan adam da kuma mutuncinsu, ya na mai cewa kamata yayi a ce su na makaranta ba komar hukuma ba. Tsohon ɗan…
