Babaji

5711 Posts

Trump da Harris sun kammala matakin ƙarshe na yaƙin neman zaɓe

Daga BELLO A. BABAJI Ƴar takarar kujerar shugaban ƙasar Amurka, Kamala Harris ta gabatar da yaƙin neman zaɓe a karo na ƙarshe, kwanaki uku kafin zaɓen ƙasar. Harris ta halarci wani shirin barƙonci ne na wani gidan telebijin a karon farko wanda an ɗauki shekaru da dama ana yi inda ƴan takarar shugaban ƙasa su kan shiga cikin shirin sakamakon shaharsa. Haka ma Tsohon shugaban ƙasar kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Donald Trump ya kammala nasa yaƙin neman zaɓen inda tuni aka fara hasashen sakamakon zaɓen. A halin yanzu jihohi bakwai ne ake ganin fafatawa za ta yi ƙarfi tsakanin…
Read More

Daga ƙarshe, matatar Ɗangote ta bayyana farashin manta

Daga BELLO A. BABAJI Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da farashin fetur ɗinta wanda ta ce za ta ke sayar da kowacce lita a Naira 990 ga motoci yayin da jiragen ruwa kuma za a ke ba su a N960. Hakan na zuwa ne bayan da ƙungiyar ƴan kasuwar fetur ta Nijeriya (IPMAN) da takwarata ta masu wuraren sayar da fetur ta Nijeriya (PETROAN) suka ce su na shigo da fetur daga waje a farashi mai sauƙi idan an kwatanta da na Ɗangote inda suka nemi da ya tattauna da masu-ruwa-da-tsaki. Saidai, matatar ta yi martani da cewa, waɗanda…
Read More

Hisbah ta tallafa wa matan da suka tuba daga harkar baɗala a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mu'assasatul Khairiyya tare da haɗin-gwiwar Hukumar Hisbah a Jihar Katsina, sun gudanar da taron yaye mata goma da suka shiriya daga harkokin baɗala tare tallafa musu don samun kafar rayuwa mai tsafta. Da yacke gabatar da jawabi a taron, Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dakta Aminu Usman Abu Ammar, ya ce matan da aka tallafa wa sun kasance daga cikin waɗanda hukumar ke kira da yi masu nasiha kan ɗabi’un rayuwa mai kyau. Ya ce, "A tsawon lokaci, hukumar Hisbah ta cigaba da yi musu wa’azi da shawara, amma sai aka ga dacewar tallafa…
Read More

Shari’ar masu zanga-zanga: Antoni-Janar na duba yiwuwar soke tuhume-tuhumen da ke kan yara marasa galihu

Daga BELLO A. BABAJI Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi ya fara ƙoƙarin neman a janye tuhume-tuhumen da ke kan matasa masu ƙarancin shekaru da aka gurfanar da su a gaban Mai Shari'a, Oboira Egwuatu a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja. Jim-kaɗan bayan hakan ne Mista Fagbemi ya karɓe ƙarar daga hannun Sufeton ƴan sanda, kamar yadda ya shelanta cikin wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a. Ya ce, akwai abeben da ofishinsa ya ke son yin nazari akai game da shari'ar kafin ya bayyana matsayarsa. Ministan ya ce ba huruminsa bane na ya soke hukuncin kotun…
Read More

Shettima ya ƙaddamar da majalisar kula da ambaliya, zaizayar ƙasa da sauyin yanayi

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ƙaddamar da majalisar kula da ambaliya da zaizayar ƙasa da fari da gandun daji (NFEDDMC). Majalisar za ta tabbatar da samar da tsari na warware matsalolin da ke tattare da sauyin yanayi da wasu nau'ukan annoba tare da aiki da hukumomin gwamnati da shiyyoyi. A lokacin da ya ke magana yayin ƙaddamarwar a Fadar shugaban ƙasa, Shettima ya ce akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa kan ƙalubalen da al'umma ke fuskanta na tasirin iftila'i da ke faruwa akai-akai a Nijeriya. Samar da majalisar ya biyo bayan shawarwari da aka samu a…
Read More

‘Yar Nijeriya ta zama baƙar fata ta farko da ta lashe shugabancin jam’iyyar Conservative a Ingila

Daga BELLO A. BABAJI Tsohuwar Sakatariyar Kasuwanci ta ƙasar Ingila, Kemi Badenoch ta zama sabuwar shugabar jam'iyyar Conservative bayan doke Robert Jenrick da ta yi a zagaye na ƙarshe a zaɓen da suka kara a ƙasar. Badenoch, wacce ta girma ne a Nijeriya, ta zama baƙar mace ta farko da ta samu shugabancin babbar jami'yya a ƙasar Turai. Za ta karɓi ragamar jagorancin jam'iyyar ne inda za ta gaji Rishi Sunak bayan ta samun ƙuri'u 53,806 inda abokin karawarta, Jenrick ya samu ƙuri'u 41,388. Tsohon Sakataren Shari'a, Robert Buckland ya ce Misis Badenoch ƙwararriya ce da za a ji dadin…
Read More

Za a iya gurfanar da ɗan shekara 7 a Nijeriya, cewar Rundunar ‘Yan Sanda

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda ta ce duk wanda ya haura shekara 7 ya cancanci a maka shi kotu. Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya faɗi hakan a ranar Juma'a yayin wata hira da gidan talabijin na 'channels' inda ya bayyana hukuncin doka da ya bada damar kai wanda ya haura shekara bakwai kotu tare da bin hanyoyin da dokar ta tsara. Kakakin ya bayyana hakan ne yayin da ake tsaka da cecekuce game da batun kama wasu yara da ake zargin su da hannu a laifukan haddasa tashin-tashina a lokacin da aka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta saki kuɗin da ma’aikatan jami’o’i ke bin ta

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta saki wasu kuɗaɗe don biyan albashin da ake bin ta na mambobin ƙungiyar ma'aikatan jami'o'i (NASU) da kuma na ma'aikatan da suka yi ritaya da ke karɓar fansho. Daraktan yaɗa labarai na ofishin Akanta-Janar na Ƙasa, Bawa Mokwa ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar inda ya ce tuni an fara biyan mambobin na NASU. Ya ce Gwamnatin Tarayya na cigaba da ƙoƙarin samar da walwala acikin ma'aikata da waɗanda suka yi ritaya a Nijeriya. A ranar Litinin ne kwamitin haɗaka na ƙungiyoyin SSANU da NASU suka shiga yajin aikin…
Read More

TCN ya dawo wuta a layin lantarki na Gombe-Damaturu-Maiduguri

Daga BELLO A. BABAJI Kamfanin Raba Wutar lantarkin Nijeriya, TCN ya ce ya kammala gyara layin 330kV na lantarki da ke bai wa Gombe-Damaturu-Maiduguri wuta. Kakakin kamfani, Ndidi Mbah ya ce an kammala gyaran ne tsakanin ranakun Laraba da Alhamis. Hakan na zuwa ne bayan sama da wata guda da layin lantarkin ya lalace wanda ba a samu gudanar da aikinsa ba a cikin ƙankanin lokaci kasancewar akwai layin Ugwuaji-Apir da shi ma ya samu matsala wanda duk hanyarsu ɗaya ce. TCN ya yi kira ga al'umma da su yaƙi ayyukan lalata wutar lantarki don samun ɗorewarsa a Nijeriya ta…
Read More