Daga BELLO A. BABAJI
Kamfanin Raba Wutar lantarkin Nijeriya, TCN ya ce ya kammala gyara layin 330kV na lantarki da ke bai wa Gombe-Damaturu-Maiduguri wuta.
Kakakin kamfani, Ndidi Mbah ya ce an kammala gyaran ne tsakanin ranakun Laraba da Alhamis.
Hakan na zuwa ne bayan sama da wata guda da layin lantarkin ya lalace wanda ba a samu gudanar da aikinsa ba a cikin ƙankanin lokaci kasancewar akwai layin Ugwuaji-Apir da shi ma ya samu matsala wanda duk hanyarsu ɗaya ce.
TCN ya yi kira ga al’umma da su yaƙi ayyukan lalata wutar lantarki don samun ɗorewarsa a Nijeriya ta hanyar ruwaito duk wani abin da zai haifar wa ɓangaren da tsaiko.