Daga BELLO A. BABAJI
Antoni-Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ya fara ƙoƙarin neman a janye tuhume-tuhumen da ke kan matasa masu ƙarancin shekaru da aka gurfanar da su a gaban Mai Shari’a, Oboira Egwuatu a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja.
Jim-kaɗan bayan hakan ne Mista Fagbemi ya karɓe ƙarar daga hannun Sufeton ƴan sanda, kamar yadda ya shelanta cikin wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a.
Ya ce, akwai abeben da ofishinsa ya ke son yin nazari akai game da shari’ar kafin ya bayyana matsayarsa.
Ministan ya ce ba huruminsa bane na ya soke hukuncin kotun da ta yi na ɗage sauraron ƙarar zuwa watan Janairu.
Wata majiya ta ce tuni Sufeton ya miƙa takardar ƙarar ga Antonin kamar yadda ya buƙata wanda kuma har ya fara aikin akai.
Majiyar ta kuma ce za a sake zama wannan satin, saɓanin 25 ga watan Janairu, 2025 da alƙalin ya ayyana da farko.
Jami’in tsaron da ke kula da ɓangaren mutum 119 da ke kare ƙarar, Marshall Abubakar ya tabbatar da cewa tuni aka fara ɗaukar matakan sauke tuhume-tuhumen da ake yi akan yaran bayan da ƙarar kai ga Antonin.