Babaji

5711 Posts

Kotu ta dakatar da CBN daga rufe asusun kuɗaɗen ƙananan hukumomi a Kano

Daga BELLO A. BABAJI Babbar Kotun Kano ta bada umarnin dakatar da babban bankin Nijeriya (CBN), da Antoni-Janar na Ƙasa (AGF) da Hukumar Kasafin Kuɗin Haraji (RMAFC) daga riƙe kuɗin wata-wata na ƙananan hukumomi 44 dake faɗin jihar. Hakan na zuwa ne bayan da Shugaban Ƙungiyar Ma'aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE), Ibrahim Muhammed da wasu ƴan jihar guda biyar da suka haɗa da; Ibrahim Shehu, Ibrahim Abubakar, Usman Isa, Sarki Kurawa da Malam Usman Imam suka shigar da ƙarar a ranar 1 ga watan Nuwamba. Waɗanda suka shigar da ƙarar sun koka ne game da cewa akwai yiwuwar ake…
Read More

Tinubu ya taya Trump murna bayan lashe zaɓen Amurka

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Shugaba Donald Trump murna bayan sake zaɓan sa da aka yi karo na biyu a matsayin shugaban ƙasar Amurka na 47. Shugaba Tinubu ya ce ya na ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Amurka duk da ƙalubalen damanmaki da duniyar yau ke ciki, ya na mai cewa haɗin kai a harkar tattali, inganta zaman lafiya da matsalolin da ke addabar al'ummar ƙasashen biyu su ake neman a samarwa mafita. Ya ce, nasarar da Trump ya samu ta nuna yadda al'ummar ƙasar suka yarda da shugabancinsa inda ya taya…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Trump ya yi wa Kamala Haris fintinkau a zaɓen Amurka

Daga BELLO A. BABAJI Ɗan takarar jam'iyyar Republican a zaɓen Amurka, Donald Trump ya kere matakin adadin ƙuri'un masu zaɓe na 270 da ake so ɗan takarar ya samu wajen lashe zaɓen 2024. Trump ya doke abokiyar ƙarawarsa ta jam'iyyar Democrats, Kamala Harris ne bayan samun ƙuri'un zaɓe 277 wanda hakan ya ba shi damar samun gurbin zama shugaban ƙasar na 47. Ɗan takarar na Republican ya samu yin nasara a manyan jihohi da suka haɗa da; Arewacin Carolina, Georgia, Pennsylvania da Wisconsin. Sauran sune; Indiana, Kentucky, Yammacin Virginia, Florida, Tennessee, Kudancin Carolina, Oklahoma, Mississippi, Alabama, Texas, Iowa da dai…
Read More

Tashar lantarki ta sake lalacewa a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Tashar raba Wutar Lantarkin Nijeriya ta sake lalacewa a wani karo bayan gyara ta da aka yi a makon da ya gabata. A ƙarshen watan Oktoba ne aka gyara ta bayan lalacewa da ta yi har sau uku. Wannan shi ne karo na tara da hakan ke faruwa a Nijeriya cikin shekarar 2024. Zuwa lokacin rubuta wannan labarin, Kamfanin Raba Wutar lantarki a Nijeriya (TCN) bai ce komai ba game da batun yayin da al'umma da dama suka kasance cikin duhu. A watan Fabrairu ne aka samu lalacewarta a karo na farko. A watan Oktoba ne…
Read More

‘Yan sanda za su binciki yadda aka tsare yaran zanga-zanga cikin ƙasƙanci

Daga BELLO A BABAJI Sufeton ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya gayyaci manyan jami'ai da suka haɗa da DCs da CID da jagororin cibiyoyin bincike kan irin kulawar da aka bai wa yara marasa galihu da aka tsare su a hannun ƴan sanda. Hakan zuwa ne bayan gabatar da yaran da aka yi cikin mawuyacin hali a ranar Juma'a, a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja. Masu zanga-zangar sun kasance cikin halin rashin samun isasshen abinci bayan watanni uku da aka tsare su wanda hakan ya haifar da cecekuce acikin al'ummar Nijeriya. Wata sanarwa da Kakakin ƴan sandan, Muyiwa Adejobi ya fitar,…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta soke aikin titin Abuja-Kaduna bayan Julius Berger ya ƙi bada haɗin-kai

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta soke aikin babbar hanyar Abuja-Kaduna-Zaria-Kano na ɓangaren Abuja-Kaduna daga hannun kamfanin Julius Berger. Daraktan watsa labarai na Ma'aikatar Ayyuka, Mohammed Ahmed ya bayyana hakan cikin wata takarda da ya fitar inda ya ce hakan ya faru ne sakamakon ƙin bada haɗin-kai da kamfanin ya yi a yayin wata ganawa da gwamnati wadda ta ce za ta bada Naira biliyan 740 ga aikin wanda kamfanin ya ƙi amincewa. An yi hukuncin ne bayan tsawon lokaci da aka ɗauka ba tare da samun wani ci-gaba ba a yayin aikin daga kamfanin. A shekarar 2018 ne…
Read More

An fara kaɗa kuri’a a Amurka don zaɓen sabon shugaban ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI A yau Talata ne ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Amurka inda al'umma ke fatan samu sabon Shugaba tsakanin Donald Trump da Kamala Harris. Harris ita ce ƴar takarar jam'iyyar Democrats bayan da shugaban ƙasar, Joe Biden ya janye daga tsayawa takarar, wadda ta kasance mai neman a bada ƴancin zubar da ciki da neman a sauƙaƙe farashin kayan abincin da na gidaje ga ma'aikata. Trump kuma a nasa ɓangaren ya yi alƙawarin rufe kan iyaka da kuma rage kuɗin haraji da kaso mai tsoka. Tsohon shugaban ƙasar ya kuma tsallake harin mutuwa har sau biyu…
Read More

EFCC ta kama tsohon abokin takarar Atiku, Okowa kan zargin badaƙala

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an hukumar EFCC sun cika hannu da tsohon Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa kan zargin sauya akalar Naira Tiriliyon 1.3 daga asusun Gwamnatin Tarayya waɗanda ke wakiltar kaso 13 na kuɗin asusun daga 2015 zuwa 2023. A ranar Litinin ne aka kama tsohon gwamnan, a Fatakwal babban birnin Jihar Ribas a lokacin da ya amsa gayyatar hukumar a offishinta dake birnin kan al'amarin. Ana zargin Okowa ne da ƙin bada asusun da aka ware don sanya kuɗaɗen, sannan da kuma wasu biliyan 40 na hannun jarin da ya mallaka a ɓangaren gas na 'UTM Floating Liquefied…
Read More

Zanga-zanga: Tinubu ya umarci a gaggauta sakin yara marasa galihu

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci a gaggauta sake baki ɗaya yaran da aka tsare waɗanda ke fuskantar hukuncin kotun kan zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a watan Agusta. Wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa, ya ce Shugaba Tinubu ya kuma umarci Ministan Jin-ƙai da ya tabbatar da bai wa yaran kulawar da ta dace. Ministan Labarai, Mohammed Idris ya bayyana hakan wa manema labarai a Fadar shugaban ƙasa dake Abuja. Shugaban ƙasar ya kuma ce a binciki baki ɗaya hukumomin da ke da hannu akan kamawa tsarewa da kuma binciken yaran, ya na…
Read More

Zamfara ta zama jiha mafi bunƙasa ta fuskar tara haraji

Daga BELLO A. BABAJI Jihar Zamfara ta zama wacce ke kan gaba a Nijeriya wajen tara haraji a bisa nazarin 'State's performance', bayan fitar da wani rahoton harajin jihohi da aka yi wa laƙabi da BudgIT's State of States Report 2024. Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa hauhawar da ɓangaren tara harajin jihar ya yi da kaso 240.44 ya faru ne sakamakon ƙin dogara da Kwamitin Kasafin Asusu na Ƙasa (FAAC) kaɗai da jihar ta yi. Rahoton, cikin nazarinsa na shekara, ya duba aikin harajin baki ɗaya jihohi 36 na Nijeriya, inda Zamfara daga mataki na 36…
Read More