Zanga-zanga: Tinubu ya umarci a gaggauta sakin yara marasa galihu

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci a gaggauta sake baki ɗaya yaran da aka tsare waɗanda ke fuskantar hukuncin kotun kan zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a watan Agusta.

Wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa, ya ce Shugaba Tinubu ya kuma umarci Ministan Jin-ƙai da ya tabbatar da bai wa yaran kulawar da ta dace.

Ministan Labarai, Mohammed Idris ya bayyana hakan wa manema labarai a Fadar shugaban ƙasa dake Abuja.

Shugaban ƙasar ya kuma ce a binciki baki ɗaya hukumomin da ke da hannu akan kamawa tsarewa da kuma binciken yaran, ya na mai cewa duk wanda aka samu da laifi, to za a ladabdtar da shi.