Kotu ta dakatar da CBN daga rufe asusun kuɗaɗen ƙananan hukumomi a Kano

Daga BELLO A. BABAJI

Babbar Kotun Kano ta bada umarnin dakatar da babban bankin Nijeriya (CBN), da Antoni-Janar na Ƙasa (AGF) da Hukumar Kasafin Kuɗin Haraji (RMAFC) daga riƙe kuɗin wata-wata na ƙananan hukumomi 44 dake faɗin jihar.

Hakan na zuwa ne bayan da Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE), Ibrahim Muhammed da wasu ƴan jihar guda biyar da suka haɗa da; Ibrahim Shehu, Ibrahim Abubakar, Usman Isa, Sarki Kurawa da Malam Usman Imam suka shigar da ƙarar a ranar 1 ga watan Nuwamba.

Waɗanda suka shigar da ƙarar sun koka ne game da cewa akwai yiwuwar ake samun jinkiri ko riƙe kuɗaɗen shugabancin ƙananan hukumomi.

Cikin waɗanda aka shigar ƙarar akwai AGF a matsayi na 45 da CBN wanda ke na 46, sai RMAFC na 47. Sauran sun haɗa da bankunan UBA da Access da wasu bankunan ƴan kasuwa guda shida.

Alƙalin Kotun ya kuma umarci masu shigar da ƙarar da su bi tsare-tsaren kotun wajen tabbatar da ingancin takardun da suka gabatar.

Daga nan ne ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga watan Nuwamba.