Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Wata tirela ta kife a jiya ranar kasuwar Shuwarin a daidai lokacin da kasuwar take tsakiyar ci, ta halaka mutane biyu ta kuma murƙushe jakuna 40.
Motar mai lamba kamar haka NGU 498XA ta ƙwace a hannun direban a lokacin da yake ƙoƙarin yin wani hawa kusa da gadar Sama dake daf da kasuwar ta Shuwarin, amma direban ya kasa sarrafata ta faɗi a ƙasa wanwar.
Tirelar tana ɗauke da jakuna kamar 100 da dawaki wadda ta taso daga Fataskum zuwa Enugu, wanda wani mai suna Muhd Hassan ya ke tuƙawa ta ƙwace aka Sami haɗarin da mace macen dabbobin.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Jigawa Lawan Shisu Adam ya tabbatar da faruwar labarin, yace a cikin waɗanda suka mutu akwai mace ɗaya da namiji ɗaya khalifa Adamu ɗan shekara 30 da kuma wata mata mai suna Innani Abubakar dukkansu sun taso ne daga Fataskum ta Jihar yobe.
Kamar yadda bayanan ‘yan sanda ya nuna direban motar ya sami guntulewar hannu yanzu haka yana kwance a asibitin Malam Aminu Kano likitoci suna ƙoƙarin ceto ransa.
Ya ƙara da cewar daga cikin jakuna 100 da aka lodawa motar guda 40 ne suka mutu yayin da sauran jakunan a Ka sakesu a garfen titi suke kiwo.