Tinubu ya sanar da rasuwar hafsan sojojin Nijeriya, Lagbaja, a hukumance

Shugaba Bola Tinubu ya sanar da rasuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, babban hafsan sojojin Ƙasa, wanda ya rasu yana da shekara 56.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa Lagbaja ya rasu ne da daren Talata a birnin Legas, bayan fama da rashin lafiya.

An haifi Lagbaja a ranar 28 ga watan Fabrairu, 1968. Shugaba Tinubu ne ya naɗa shi a matsayin babban Hlhafsan Slsojojin Ƙasa a ranar 19 ga watan Yuni, 2023. “Ya fara aikin soji ne tun bayan shiga makarantar horas da sojoji ta NDA a shekarar 1987,” in ji shugaban ƙasa. “A ranar 19 ga watan Satumba, 1992 aka ɗauke shi a matsayin Laftanar a sashen Infantry na Nijeriya, a matsayin ɗan ajin 39.”

Gaba ɗaya a cikin aikinsa, Laftanar Janar Lagbaja ya nuna gwanintarsa da ƙwarewa, inda ya yi aiki a matsayin mai jagorantar runduna a bataliya ta 93 da kuma bataliya ta 72 ta sojojin na musamman. Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Laftanar Janar Lagbaja ya kasance jarumi mai ƙwarin gwiwa da ƙoƙari wajen kare ƙasa.

Shugaban ya miƙa ta’aziyya ga iyalansa da dukkan rundunar sojojin Nijeriya a wannan lokaci mai raɗaɗi. Ya kuma yi addu’ar samun rahama ga Laftanar Janar Lagbaja tare da yabawa da gagarumin gudunmawar da ya bayar ga ƙasa.