Gwamnan Kaduna ya yaba wa Shugaba Tinubu kan sakin yara masu zanga-zanga

Daga IBRAHIM IMAM IKARA

A ranar Talata ne Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya marabci yaran jihar daga Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima bayan umarnin Shugaba Tinubu kan a gaggauta sakin su ba tare da sharaɗi ba.

Malam Uba Sani ya bayyana a shafinsa na kafafen sada zumunta cewa mataimakin shugaban ƙasa ne ya ba shi yaran bayan janye tuhumar da ake yi musu na cin amanar ƙasa a zanga-zangar watan Agusta, 2024.

Yaran sun bayyana wa gwamnan cewa, wasu ne suka yi amfani da su wurin haifar da gagarumin tashin hankali a Kaduna ma Nijeriya, sakamakon haka ne gwamnatin jihar za ta tallafa wa ɗalibai daga cikinsu don su koma makaranta yayin da waɗanda ke da ƙwarewa a sana’o’i kuma za a tallafa musu da kayan aiki.

Gwamnan ya ce yaran sun tabbatar ma sa da cewa daga yanzu za su kasance masu kyawawan halaye domin zama jakadu na gari ga jihar, sannan gwamnatin jihar za ta haɗa kan iyaye da masu kula da yaran domin samar da tsarin gyaran da zai dace da yaran.

Gwamnan ya kuma yi godiya ta musamman ga Shugaba Tinubu kan umarnin gaggawa da ya bayar na sakin su ba tare da sharaɗi ba.

Kazalika, gwamnan ya yi godiya ga mataimakin shugaban ƙasa na miƙa yaran zuwa ga gwamnatin jihar cikin sauƙi tare da gode wa sauran ƴan ƙasa masu kishi.