Tashar lantarki ta sake lalacewa a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI

Tashar raba Wutar Lantarkin Nijeriya ta sake lalacewa a wani karo bayan gyara ta da aka yi a makon da ya gabata.

A ƙarshen watan Oktoba ne aka gyara ta bayan lalacewa da ta yi har sau uku.

Wannan shi ne karo na tara da hakan ke faruwa a Nijeriya cikin shekarar 2024.

Zuwa lokacin rubuta wannan labarin, Kamfanin Raba Wutar lantarki a Nijeriya (TCN) bai ce komai ba game da batun yayin da al’umma da dama suka kasance cikin duhu.

A watan Fabrairu ne aka samu lalacewarta a karo na farko.

A watan Oktoba ne Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu ya ce, tsaiko da tashar ke samu, abu ne da ba za a iya kauce masa ba sakamakon yanayin kayayyakin lantarkin ƙasar.

Ya ce akwai buƙatar kowacce shiyya a Nijeriya ta samu tashar lantarkinta wanda hakan ne zai tabbatar da samun tsayuwar lantarki ba tare da samun tsaiko akai-akai ba.

Ya ce, kasancewar da layin lantarki ɗaya baki ɗaya jihohin Nijeriya 36 suka dogara ya sa hakan ke faruwa, inda samun ƙaruwar tashoshi a shiyyoyin ƙasar za su taimaka wajen rage aukuwar lamarin.