Babaji

5710 Posts

‘Yan bindiga sun kashe mutane 15 a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Aƙalla mutane 15 ne suka rasu a wani ba-takashi tsakanin waɗansu mutane da ake sa ran Lukurawa ne da ke alaƙa da ISWAP da suka fito daga yankin ƙasashen waje kuma su ke da'awar musulunci, da kuma al'ummar garin Mera da ke ƙaramar hukumar Mulki ta Augie. Lamarin ya auku ne a Juma'a da rana bayan da maharan suka kora ilahirin dabbobin mutanen ƙauyen. Wakilinmu ya ruwaito cewa, bayan maharan sun ƙwace dabbobin daga mai kiwon ne shi kuma ya shiga gari ya faɗa wa mutanen garin inda su kuma daga nan sai suka fito…
Read More

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da wani sahun jami’an community watch corps a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da ɗauka da horas da kashi na biyu na jami'an community watch corps domin faɗaɗa ayyukan tsaro a faɗin jihar. A ranar Alhamis da ta gabata ne ƴan ta'adda suka kashe jami'ansu biyar yayin da kuma suka samu raunuka a ƙaramar hukumar Jibiya. Da ya ke jawabi a wajen bikin yaye jami'an, Gwamna Dikko Raɗɗa, ya ce jami'an za su taimaka wa sauran jami'an tsaro wajen yaƙi da ta'adanci a faɗin jihar. Ya ce jami'ai 1,466 gwamnatin jihar ta ɗauka aiki shekarar da ta gabata waɗanda su na cigaba da…
Read More

Babban koma-baya ga PDP: Tsohon ɗan majalisa a Zamfara, Kabiru Classic ya koma APC

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Kabiru Yahaya Classic ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Classic ya bayyana sauya shekar tasa ne a ranar Alhamis, bayan ganawa da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Tukur Ɗanfulani da Tsohon shugaban APC na jihar, Alhaji Lawal M. Liman da sauran masu-ruwa-da-tsaki na jami'iyyar. Yahaya Classic ya wakilci mazaɓar Anka/Talata Mafara tsakanin 2019 zuwa 2023 a karkashin PDP a mataki na Majalisar Wakilai. Tsohon ɗan majalisar ya ce, ya fice daga PDP ne saboda babu adalci a jam’iyyar reshen jihar shi ya sa ya yanke shawarar ficewa daga…
Read More

Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da tashoshin KTSTA a Mashi da Ingawa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da sabbin tashoshi na hukumar sufuri ta jihar, KTSTA, a ƙananan hukumomin Mashi da Ingawa. A wajen ƙaddamar da tashoshin da aka yi a manyan ofishin ƙananan hukumomi biyun, Gwamna Raɗɗa ya ce tashoshin za su zama wuraren ajiye motoci da ɗibar fasinjoji daga ƙananan hukumomin biyu har ma da maƙotansu. Ya ce, faɗaɗa ayyukan KTSTA zuwa wasu sassan jihar na da nufin sauƙaƙa sufuri ga al'umma a yanayin hauhawar farashin man fetur da ake ciki. Duba da hakan yasa hukumar ke yin rangwame ga matafiya…
Read More

Zaɓen Amurka: Abin da Obama ya ce bayan nasarar Trump

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Barack Obama ya taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Donald Trump murna bisa nasarar da ya samu. Obama da matarsa, Michelle cikin wani saƙon gamayya, sun ce lallai ba su yi tsammanin haka sakamakon zaɓen zai kasance ba la'akari da rashin jituwa da ke tsakanin su da jam'iyyar Republican. "Amma kasancewar a tsarin demokraɗiyya ake rayuwa wanda ba a kodayaushe ra'ayinmu ne zai yi nasara ba, ya sa mu karɓar miƙa mulki cikin salama." Amurka ta kasance ƙasa ce wadda a ƴan shekarun nan ake samun sauye-sauye musamman a ɓangaren hauhawar farashin kayayyaki da…
Read More

Remi Tinubu da matar Shettima sun je ta’aziyyar rasuwar Janar Lagbaja a Legas

Daga BELLO A. BABAJI Matar shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu ta je gaisuwar ta'aziyyar rasuwar shugaban sojojin ƙasa, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja. Matar mataimakin shugaban ƙasa, Hajiya Nana Shettima da ta mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA), Hajiya Ribaɗu. Matar Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Misis Oghogho Musa ita ta tarbe su. A lokacin da ta ke jajenta wa iyalan mamacin, Remi Tinubu ta yi kira gare su da su kasance masu haƙuri tare da kwaikwayon kyawawan halayen da ya bari. Ta nemi ƴaƴan marigayin da su tsayu wajen cimma kyawawan manufofinsu na rayuwa. Janar Lagbaja ya mutu…
Read More

Jamus ta buƙaci Isra’ila ta bari a kai kayan tallafi Arewacin Gaza

Daga BELLO A. BABAJI Ƙasar Jamus dake Nahiyar Turai ta yi kira ga Isara'ila da ta bari a kai ƙarin kayan agaji na jinƙai zuwa Arewacin Gaza a ƙasar Palestine. Kakakin Ma'aikatar waje ta Jamus ya bayyana hakan a inda ya ce, "Mu na kiran gaggawa ga Gwamnatin Isra'ila ta yi abin da yake wajibi ne a kanta ƙarƙashin dokar ƙasa-da-ƙasa." Jakadan Palestine a Nijeriya, Abdallah Abu Shawesh ya ce watanni 13 kenan da ake cigaba da buɗe wuta da tarwatsa garuruwa da hana a kai kayan tallafi ga Falasɗinawa. Ya ce, su na kira ga Jamus da ta daina…
Read More

Gwamnan Zamfara ya dakatar da cire kuɗaɗe ba bisa doka ba a albashin ma’aikata a jihar

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya umarci a gaggauta dakatar da duk wasu rage-rage da ake yi wa albashin ma'aikata ba bisa ƙa'ida ba a jihar. Hakan na zuwa ne bayan da ma'aikata suka yi ta gabatar da ƙorafe-ƙorafe game da rage-rage da ake samu daga ofishin biyan albashi na jihar. Cikin wata takarda da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, Dauda Lawal ya ce ya ɗauki matakin ne don tabbatar da inganci ga ɓangaren kula da albashin ma'aikatan sakamakon haramtattun hanyoyi da ake bi wajen zaftare musu kuɗaɗe. Gwamnan ya kuma umarci kwamishinan kuɗi da…
Read More

Gwamnan Kaduna ya yaba wa Shugaba Tinubu kan sakin yara masu zanga-zanga

Daga IBRAHIM IMAM IKARA A ranar Talata ne Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya marabci yaran jihar daga Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima bayan umarnin Shugaba Tinubu kan a gaggauta sakin su ba tare da sharaɗi ba. Malam Uba Sani ya bayyana a shafinsa na kafafen sada zumunta cewa mataimakin shugaban ƙasa ne ya ba shi yaran bayan janye tuhumar da ake yi musu na cin amanar ƙasa a zanga-zangar watan Agusta, 2024. Yaran sun bayyana wa gwamnan cewa, wasu ne suka yi amfani da su wurin haifar da gagarumin tashin hankali a Kaduna ma Nijeriya, sakamakon haka ne gwamnatin…
Read More

Kotu ta dakatar da CBN daga rufe asusun kuɗaɗen ƙananan hukumomi a Kano

Daga BELLO A. BABAJI Babbar Kotun Kano ta bada umarnin dakatar da babban bankin Nijeriya (CBN), da Antoni-Janar na Ƙasa (AGF) da Hukumar Kasafin Kuɗin Haraji (RMAFC) daga riƙe kuɗin wata-wata na ƙananan hukumomi 44 dake faɗin jihar. Hakan na zuwa ne bayan da Shugaban Ƙungiyar Ma'aikatan Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (NULGE), Ibrahim Muhammed da wasu ƴan jihar guda biyar da suka haɗa da; Ibrahim Shehu, Ibrahim Abubakar, Usman Isa, Sarki Kurawa da Malam Usman Imam suka shigar da ƙarar a ranar 1 ga watan Nuwamba. Waɗanda suka shigar da ƙarar sun koka ne game da cewa akwai yiwuwar ake…
Read More