‘Yan bindiga sun kashe mutane 15 a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Aƙalla mutane 15 ne suka rasu a wani ba-takashi tsakanin waɗansu mutane da ake sa ran Lukurawa ne da ke alaƙa da ISWAP da suka fito daga yankin ƙasashen waje kuma su ke da’awar musulunci, da kuma al’ummar garin Mera da ke ƙaramar hukumar Mulki ta Augie.

Lamarin ya auku ne a Juma’a da rana bayan da maharan suka kora ilahirin dabbobin mutanen ƙauyen.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, bayan maharan sun ƙwace dabbobin daga mai kiwon ne shi kuma ya shiga gari ya faɗa wa mutanen garin inda su kuma daga nan sai suka fito da makamai suka tunkare su inda aka yi arangama.

Bayanai sun nuna cewa an kashe mutane 15 daga cikin ƴan Mera yayin da waɗansu kuma suka samu raunuka,

Haka su ma maharan an kashe waɗansu daga cikin su, sai dai sun tafi da gawawwakin waɗanda aka kashe da waɗanda aka yi wa raunuka.

Mataimakin gwamnan Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida a madadin gwamnan jihar, ya je garin da tare da kwamishinan ƴan sanda da sauran jami’an tsaro tare da Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera inda ya jajenta musu tare da shaida musu da cewa gwamnati ba za ta ƙyale irin waɗannan abubuwa suna faruwa ba da yardar Allah za a ɗauki matakin da ya dace.

Kazalika, Mai Martaba Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ya ce mutanen da suka rasu ba su mutu a banza ba inda ya ce shahada suka yi, saboda sun mutu ne wajen kariyar dukiyarsu.

Ya yi kira ga al’umma da su tashi tsaye su kare kawunansu, ya na mai cewa kar su jira sai jami’an tsaro sun zo a duk lokacin da irin hakan ya faru.

Wani mazaunin Mera ya bayyana wa wakilinmu da cewa, yankin nasu ya daɗe yana fuskantar matsalolin ƴan ta’adda, kama daga ɓarayin dabbobi zuwa masu garkuwa da mutane domin neman karɓar kuɗin fansa, sai dai yanzu abin ya yi sauƙi saboda matakan kare kai da suka ɗauka.

Sanata Yahaya Abdullahi mai wakiltar mazaɓar Kebbi ta Arewa ya aika da saƙon ta’aziyya tare da jajentawa ga al’ummar yankin.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su tsaurara matakan tsaro musamman a waɗannan yankunan da waɗannan ƴan bindigar ke yi wa barazana.