Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya ce nan ba da jimawa ba zai cire wasu daga cikin mambobin Majalisar Zartarwa da aka tantance ƙwazonsu a ƙarƙashin ayyukansu .
Gwamnan, wanda ya tabbatar da karɓar rahoton kwamitin duba aikin mambobin majalisar, ya bayyana cewa al’umma za su ji matakin da gwamnatinsa za ta ɗauka nan ba da jimawa ba.
Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya faɗi hakan a cikin wata sanarwa da ya aika wa kadaura24.
Gwamnan ya tunatar da al’umma game da shirin sauya wasu daga cikin mambobin majalisar a wata hira kai-tsaye da aka yi da shi ta gidan rediyo da wasu kafofin yaɗa labarai da aka gudanar a Gidan Gwamnatin jihar a ranar Laraba.
Ya kuma ce tsawon shekara ɗaya da rabi kenan da ake nazarin ƙwarewarsu, don haka zai yanke hukuncin ƙarshe game da su.
Ya ƙara da cewa, babu ɗaya daga cikin kwamishinonin da suka riƙa neman muƙamin inda ya jaddada cewa kafin naɗin su, ya yi la’akari da ƙwarewa, amana, da kuma shawara daga mashawarta.
Har’ilayau, Gwamna Abba ya ce abin da ya ke buƙata daga kwamishinoni shi ne su kasance masu biyayya gare shi, ga jam’iyyar NNPP, da kuma tafiyar Kwankwasiyya tare da jajircewa a kan ayyukansu da kuma kawo sabbin dabaru don cigaban jihar.