Babban Hafsan Tsaro ya jinjina wa sojoji kan wanke jami’ansu bisa zargin zubar da ciki a Arewa-maso-Gabas

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya yaba wa sakamakon da Tawagar Bincike ta Musamman ga Tauye Haƙƙin Ɗan-adam a ƙoƙarin shafe Ayyukan Ta’addanci a Arewa-maso-Gabas ta fitar, wanda ya wanke jami’an sojoji daga zargin zubar da ciki da adadinsu ya kai 10,000 a yankin.

Tawagar, wadda ta ɗauki tsawon shekaru biyu ta na bincike game da lamarin, ta miƙa rahotonta ga Hukumar ƙare ƴancin Ɗan-adam (NHRC) a hedikwatarta da ke Abuja, a ranar Juma’a.

Rahoton ya ce, tabbas abin da ake tuhumar sojojin na bin wasu hanyoyi don zubar da ciki da duka da fyaɗe da ma wasu kashe-kashe, ƙarya ce.

Cikin wata takarda da Daraktan Labarai na Hedikwatar Tsaro, Burgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, Janar Musa ya yaba wa tawagar ta mutane bakwai bayan da kwamitin ƙasa-da-ƙasa na ƙungiyar Red Cross ya nemi a binciki batun talasta wa mata zubar da ciki da wasu nau’ukan tauye haƙƙi da aka ce sojoji na yi a Arewa-maso-Gabas.

A watan Maris na 2023 NHRC ta samar da tawagar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Abdu Aboki (rtd) don yin bincike kan lamarin.

Janar Musa ya kuma jaddada ƙoƙarin dakarun tsaron Nijeriya wajen kare ƴancin Ɗan-adam da tabbatar da tsaro a ƙasar.

Har’ilayau, Hilary Ogbonna wata babbar Mai bada shawara ce a NHRC, wadda ta bayyana cewa, babu wata hujja da ke iya tabbatar da zargin acikin rahoton.

A watan Disambar 2022 ne ‘Reuters’ ta fitar da wani rahoto da ke zargin sojoji da tauye haƙƙin ɗan-adam ta hanyar tilasta wa mata zubar da ciki da wasu nau’ukan cutarwa waɗanda sojojin suka ceto su daga hannun mayaƙan Boko Haram.