

Daga BELLO A. BABAJI
Matar shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu ta je gaisuwar ta’aziyyar rasuwar shugaban sojojin ƙasa, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja.
Matar mataimakin shugaban ƙasa, Hajiya Nana Shettima da ta mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA), Hajiya Ribaɗu.
Matar Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Misis Oghogho Musa ita ta tarbe su.

A lokacin da ta ke jajenta wa iyalan mamacin, Remi Tinubu ta yi kira gare su da su kasance masu haƙuri tare da kwaikwayon kyawawan halayen da ya bari.
Ta nemi ƴaƴan marigayin da su tsayu wajen cimma kyawawan manufofinsu na rayuwa.
Janar Lagbaja ya mutu ne a ranar Talata, ya na da shekaru 56 a duniya.
