Kamala Harris ta kira Donald Trump a waya domin taya shi murna

Yar takarar shugabancin ƙasar Amurka a jam’iyyar Democrat kuma mataimakiyar shugaban ƙasa, Kamala Harris, ta kira zaɓaɓben shugaban ƙasa Donald Trump, inda ta amince da shan kaye.

Harris ta taya Trump murna kan nasarar da ya samu a zaɓen 2024, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS News ta bayyana.

A cikin kiran, Harris ta jaddada muhimmancin miƙa mulki cikin lumana da shugabanci na kowa da kowa a Amurka. An bayyana cewa za ta yi jawabi ga magoya bayanta a jami’ar Howard nan gaba.

A nasa ɓangaren, Trump ya gode wa magoya bayansa tare da yabawa ƙoƙarin da suka yi. A cikin sanarwa daga tawagar yakin neman zabensa, Trump ya bayyana nasarar tasa a matsayin wani babbar nasara ta tarihi, tare da yin alƙawarin kawo sauyi ga Amurka domin samun cigaba mai ɗorewa.