Me ake nufi da khul’i?

 

Daga AISHA ASAS 

Da yawa daga cikinmu su na jin kalmar khul’i, sai dai ba su san alaƙarta da su ba, ko kuma ma’anar ta, don haka za mu soma da bayanin ma’anar khul’i kafin mu ji hukuncin sa a Musulunci. Khul’i hukunci ne na fansar kai da mace zata iya yi a yayin da ta yi sha’awar rabuwa da mijinta.

Kamar yadda ku ka sani, hukuncin tsinke yagiyar aure na ɗaya daga cikin iko da Musulunci ya ba wa miji, hakan na nufin ba mai ikon sakin mace a take, kuma ta saku, sai mijinta, sai kuma wasu dalilai da suka ba wa alƙali damar iya raba auren.

Da wannan ne Musulunci ya yi tanadi ga mata, kasancewar sa addinin adalci, tunda bai bata ikon sakin mijinta idan ta yi muradin hakan, sai ya fito da hanyar da zata zama mafita gare ta yayin da buƙatar rabuwa ta taso ta ɓangaren ta, wato ta fanshi kanta daga wurin mijinta da ke da ikon sakinta, ta hanyar ba shi wani abu daga dukiya don ya samu damar yin wani aure cikin sauƙi. Kamar yadda aya a cikin littafi mai tsarki ta faɗa a cikin suratul Baƙara, aya ta 229, inda Allah maɗaukakin sarki ya ce, “Saki sau biyu yake, sai a riƙe shi da alkhairi, ko kuwa a sallama bisa kyautatawa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da ku ka ba su, face fa idan su (ma´auran) na tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba. Idan kun (danginsu) ji tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba, to, babu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyakokin Allah ne saboda haka kada ku ƙetare su. Kuma wanda ya ƙetare iyakokin Allah, to waɗannan su ne azzalumai.”

Idan mun ɗauki kusa da ƙarshen ayar, inda Allah ke cewa, “idan kun ji tsoron ba za su tsayar da iyakokin Allah ba, to babu laifi a kansu cikin abin da ta yi fansa da shi.” A daidai nan ne khul’i ya samu muhallinsa a addini, kuma ya samu halaccin sa.

Waɗanne dalilai ne ke sa a yi khul’i?

Yayin da mace ta ji ta tsani zama da mijinta, ta dalilin an wayi gari ta daina jin sonsa a ranta, ko ta gaji da auren bisa wani dalili na ra’ayin kanta, amma mai ƙwari, kuma tana tsoron saɓawa Allah idan ta ci gaba da zama da mijin dalilin rashin son zaman da take, ta hanyar bijirewa buƙatarsa ko kasa yi masa biyayya, ko muzgunawar da yake mata ta tsane shi ta dalilin, ko rashin gamsar da ita ba bisa ganganci ba, sai don na shi yanayi.

Ta yaya ake yin khul’i?

Hanyoyi biyu ne za a iya gina khul’i a kansu, wanda ya danganta da irin zaman da mace ke yi da mijinta. A wani lokaci, za a iya tarar da cewa, zaman lafiya ake yi tsakanin mace da mijin, sai dai rashin so ko wani dalili da ta ɗauka da muhimmanci ne kawai ke yi mata shamaki da jin daɗin zama da mijin nata. A irin wannan za su iya yin yarjejeniya tsakaninsu.

Cikin ruwan sanyi ta yi masa bayanin buƙatarta, da kuma neman fansar kanta da take yi daga aurensa. A nan za su iya tsayar da matsaya, na abinda zata ba shi a matsayin kuɗin raba aurensu. Idan har sun yi matsaya, sai su sanya shedu na daga dangi don samun tabbaci.

Hanya ta biyu ita ce ta wurin shari’a, ko malamin da ya saba yin hukuncin da ya danganci aure, hakan na samuwa idan abin na neman zama na fitina, ko mijin ya ɗauki abin da zafi, ko kuma dama ba zaman lafiya ake yi ba. Alƙalin da ta kai ƙara wurin sa, ko malamin shi zai nemo mijin, ya shiga tsakani har a kai ga matsaya.