Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. A satin da ya gabata, idan ba ku manta ba, mun ɗauko bayani kan yadda wanka ke da matuƙar muhimmanci a sha’anin kwalliya da ma tsafta bakiɗaya. Inda muka bayyana cewa, babu kwalliyar da za ta fita yadda ake so face sai da wanka, wanda wankan ba yana nufin na rana guda ba, kamar dai yadda muka bayyana.
Mun kuma kawo wa masu karatu wasu daga cikin sabulun da za a iya haɗawa don saka fata sheƙi, ko fitar da datti yadda ya kamata har ma da cire tabo ko ƙuraje.
A wannan makon ma, da yardar mai dukka, za mu ƙara wasu sabulai ne kafin mu rufe darasin.
Uwargida za ta tanadi kayan haɗi kamar haka:- Man zaitun, zuma, lemon tsami, magiji, sabulun salo, sabulun gana. Ki haɗe sabullan da magiji a dake, sai a zuba zuma, a matse lemun tsami kaɗan( kada dai a manta, kamar yadda muka faɗa a satin da ya gabata, akwai fatar da ba ta jimirin lemon tsami, ko kuma yake illata ta, kuma akwai wadda yawanshi ne ke kawo mata matsala. Don haka ki san a wane mataki fatarki take kafin amfani da shi) a zuba man zaitun, a kwaɓa su sosai su haɗe, sai a dinga wanka da shi. Wannan haɗin ya fi tasiri ga baƙar mace.
Uwargida za ta haɗa kaya kamar haka:- Sabulun dudu osun, lalle, zuma, sabulun salo, garin darbejiya, kurkum, dettol, sabulun zaitun. Ki dake sabulan, sai ki haɗa masu kayan haɗi daidai da yawan su, ki haɗe su sosai har sai sun zama ɗaya, idan ruwan su bai wadatar ba za ki iya sa ruwa kaɗan don su haɗe sosai. Wannan haɗin zai dace da ko wacce irin fata. Zai kawar da datti, sannan ya sanya fata sheƙi