Babban koma-baya ga PDP: Tsohon ɗan majalisa a Zamfara, Kabiru Classic ya koma APC

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Kabiru Yahaya Classic ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Classic ya bayyana sauya shekar tasa ne a ranar Alhamis, bayan ganawa da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Tukur Ɗanfulani da Tsohon shugaban APC na jihar, Alhaji Lawal M. Liman da sauran masu-ruwa-da-tsaki na jami’iyyar.

Yahaya Classic ya wakilci mazaɓar Anka/Talata Mafara tsakanin 2019 zuwa 2023 a karkashin PDP a mataki na Majalisar Wakilai.

Tsohon ɗan majalisar ya ce, ya fice daga PDP ne saboda babu adalci a jam’iyyar reshen jihar shi ya sa ya yanke shawarar ficewa daga cikin ta.

“Ni Kabiru Yahaya Classic, a yau Alhamis, 7 ga watan Nuwamba, 2024, ina so in sanar da ficewata daga PDP zuwa jam’iyyar Progressive Party, APC.”

“Na sauya sheƙa ne da ɗaukacin manyan jam’iyyar PDP a ƙaramar hukumar Talata Mafara da suka haɗa da EXCO na ƙaramar hukumar da shugabannin mazaɓu 10 cikin 11 na PDP”, inji Classic.

Sannan, Classic ya bayyana APC a matsayin babbar jam’iyya mai adalci da gaskiya.

Da ya ke karɓar ɗan majalisar, shugaban APC na jihar, Tukur Umar Ɗanfulani ya bayyana sauya sheƙar a matsayin wani abin farin ciki ga jam’iyyar APC.

“Mun yi farin ciki da karɓar dan uwanmu a babbar jam’iyyarmu. Wannan babban ci-gaba ne”, inji Ɗanfulani.

“Sauran masu sauya sheka daga jam’iyyar PDP da ke jagorantar gwamnati a jiharmu ta Zamfara suna shirin shiga APC nan ba da jimawa ba.”

Shugaban ƙungiyar siyasa a ofishin Sanata Abdul’aziz Yari, Alhaji Lawal M. Liman ya yaba wa Kabiru Classic da sauran waɗanda suka sauya sheƙa bisa shiga APC da suka yi.

Ya ce APC ita ce jam’iyya ɗaya tilo da ke da tsarin ciyar da Zamfara da Nijeriya gaba.

Muhimman mutanen da suka halarci taron sun haɗa da; Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Mu’azu Magarya; Coordinator na shiyyar, Sanata Abdul’aziz Yari; Alhaji Sha’aya Sarkin-Fawa Talata Mafara.

Sauran sune; Tsohon SSG na Zamfara, Alhaji Kabiru Balarabe, tsoffin Kwamishinoni da tsoffin masu mulki.

By Babaji