01
Nov
Daga BELLO A. BABAJI Yayin da ake samun cecekuce game da ƙudirorin da ke neman a yi wa haraji kwaskwarima a Nijeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ba za a janye takardar ƙudirin ba daga Majalisa. Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya bayyana hakan cikin wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, inda ya ce akwai buƙatar ƙudirin ya samu dubawa ta Majalisa. Majalisar Tattalin Arziƙi ƙarƙashin jagorancin Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ta nemi a janye batun kwaskwarimar tare da neman shawarar masu-ruwa-da-tsaki kafin gabatar da shi. Shugaba Tinubu ya yaba wa mambobin…
