Babaji

5712 Posts

An shiga murna bayan dawowar wutar lantarki a Kano

Daga BELLO A. BABAJI Al'ummar yankin Gaida dake ƙaramar hukumar Kumbotso a Jihar Kano, sun shagaltu da murna bayan dawowar wutar lantarki da aka ɗauki tsawon makonni biyu da lalacewarta. Jihohin Arewacin Nijeriya da dama sun shiga matsalar rashin wuta tun bayan tsaiko da aka samu a tashoshin lantarki na Jihohin Benue da Enugu. A farkon makon nan ne Kamfanin Raba Wutar lantarki na Ƙasa, TCN ya ce za a kammala aikin gyaran wutar a kwana biyar. A ranar Laraba ne wutar ta dawo wa jihohi huɗu da suka haɗa da; Filato, Bauchi, Gombe da Benue ƙarƙashin kamfanin raba wuta…
Read More

Babu wani yanki na sojoji da ke ƙarƙashin ƴan bindiga a Neja – Hedikwatar Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba ne Hedikwatar Tsaron Nijeriya, DHQ ta ƙaryata wani rahoto da aka jingina wa Majalisar Dokokin Jihar Neja da ke cewa sansanin horon sojoji na ƙaramar hukumar Kwantagora na ƙarƙashin ikon ƴan bindiga. Blueprint ta ruwaito cewa Majalisar ta tattauna wani batu da ke roƙon Gwamna Mohammed Umar Bago ya haɗe kai da sojoji wajen tabbatar da kora ƴan bindiga daga babban sansanin horo na sojoji dake ƙaramar hukumar. Saidai, Rundunar sojojin ta ofishin Daraktan Labaranta, Manjo-Janar Edward Buba, ta ce zargin bai tabbata ba, inda an samu ba-takashi ne a tsakanin sojoji da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisa ta tabbatar da sababbin ministoci bayan tantance su

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba ne Majalisar Dattijai ta tabbatar da Bianca Odumegu-Ojukwu a matsayin sabuwar ƙaramar Ministar Harkokin Waje. Sauran ministocin sun haɗa da; Dakta Jumoke Oduwole a matsayin Ministar Masana'antu da Kasuwanci da Ci-gaba, da Nentawe Yilwatda a matsayin Ministan Jin-ƙai da Rage Talauci da kuma Muhammadu Dingyaɗi a matsayin Ministan Ƙwadago da Ɗaukar aiki. Haka nan, ta kuma tabbatar da Idi Muktar a matsayin Ministan Ci-gaban Kiwo, sai Yusuf Ata wanda shi ne sabon Ministan Gine-gine da kuma Dakta Suwaiba Sa'id Ahmad a matsayin ƙaramar Ministar Ilimi. Sauran bayanai za su O daga baya…
Read More

Ronaldo ya zaɓi mawaƙin da ya fi so tsakanin Wizkid da Davido

Daga BELLO A. BABAJI Zakaran ƙwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo ya zaɓi mawaƙin da ya fi so' tsakanin Davido da Wizkid, waɗanda su biyun ƴan Najeriya ne. Tsohon ɗan wasan ƙungiyar Real Madrid ɗin yayin wallafa wani shiri a shafinsa na YouTube a ranar 29 ga watan Oktoba, 2024, ya samu zaɓin ɗaukar ɗaya daga cikin mawaƙan. Yayin ɗaukar wanda ya fi so, Ronaldo ya zaɓi Davido akan Wizkid. Hakan na zuwa ne yayin da ake gwabza hamayya tsakanin mawaƙan Najeriya. A baya ne Blueprint ta ruwaito inda Ronaldo ya jinjina wa waƙar Asake, wanda a ciki ya haska…
Read More

Kotu ta dakatar da Gwamnatin Tarayya daga bai wa Jihar Ribas kason kuɗi

Daga BELLO A. BABAJI Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci babban bankin Nijeriya (CBN) da ya dakatar da bai wa Jihar Ribas kason kuɗi na wata-wata da ya saba. Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta bayyana hakan a yayin hukunci kan wata ƙara da Majalisar Dokokin jihar ƙarƙashin Martins Amaewhule ta shigar. Kotun ta ce baki ɗaya kuɗin da ake bai wa gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Siminalayi Fubara daga watan Janairun 2024, abu ne wanda ya saɓa wa doka don haka wajibi ne a dakatar da shi. Haka nan, kotun ta ce kuɗin kasafi da gwamnan ya tsara akan…
Read More

NNPC ya sake ƙara farashin fetur a Abuja da Legas da wasu jihohi

Daga BELLO A. BABAJI Kimanin sati uku kenan da Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL ya ƙara kuɗin litar fetur wanda ya sa gidajen man dake ƙarƙashinsa suka sauya farashinsu daga N998 a zuwa N1,025 a Legas. Gidajen man da ke ƙarƙashin kamfanin kai-tsaye na sayarwa akan N,1025 yayin da waɗanda ke mallakar ƴan kasuwa ne ke sayarwa akan N1,100. Haka ma Abuja, kamfanin na sayarwa akan N1,060 daga N1,030 na kowacce lita tun daga ranar Talata. Tun daga lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a Nijeriya ne, farashinsa yake ta hauhawa wanda daga…
Read More

‘Yan sanda sun kama ɗaliba ƴar shekara 17 da ta yi ƙaryar an sace ta an kashe

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an ƴan sandan Jihar Imo sun yi nasarar kama wata ƴar shekara 17 mai suna Jesse Chidiebere wadda ɗaliba ce a Jami'ar jihar, IMSU wacce ta yi ƙaryar garkuwa da kuma mutuwa. Henry Okoye, wanda shi ne Kakakin rundunar ƴan sandan, ya faɗa a cikin wata sanarwa cewa sun samu rahoton zargin ɓacewar yarinyar a ranar Asabar da ta gabata. Chidiebere ta bayyana wani saƙo ta wattsapp da ke nuna cewa an yi garkuwa da ita kuma an kashe ta wanda hakan ya sa iyalanta suka garzaya ofishin ƴan sandan don isar da rahoto. Daga nan…
Read More

PRP reshen Katsina za ta maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan ɗaukewar lantarki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tsohon ɗan takarar gwamna a jam'iyar PRP, a Jihar Katsina, Alhaji Imrana Jabiru Jino ya ce zai maka Gwamnatin Tarayya a kotu kan tsawon kwanaki da aka ɗauka ba wutar lantarki a Arewacin Nijeriya. Ya ce ya shirya tattara bayanai tare da aika su ta yanar gizo ga duk iyalan mutanen da suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu sanadiyyar ɗaukewar wutar lantarki. Jino ya koka kan yadda manyan kamfanoni da ƙananan ƴan kasuwa suka tafka asara sanadiyyar rashin wutar lantarki. "Ƙananan ƴan kasuwa da suka haɗa da masu walda, aski, sayar da kayan sanyi da sauran…
Read More

Sai gwamnati da gidajen jaridu sun haɗa kai wajen ciyar da Nijeriya gaba – Shettima

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira da a ƙarfafa alaƙa tsakani gwamanti da gidajen jaridu wajen sauƙe nauyin harkokin ci-gaba a Nijeriya. Shettima ya faɗi hakan ne a ranar Talata, a lokacin da jagororin ƙungiyar editocin Nijeriya ta Nigeria Guild of Editors da suka kai masa ziyara Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, ya na mai nuna muhimmancin taimakon gwamnatin a harkokinsu. Ya ce, lokaci ya yi da ya kamata a ce an fifita shugabanci sama da siyasa don haka a haɗe kai da gidajen jaridu. Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi tsokaci game…
Read More

Fadar Shugaban ƙasa ta ɗage tantance sababbin ministoci

Daga BELLO A. BABAJI Fadar Shugaban ƙasa ta dakatar da batun tantance sabbin ministoci bakwai da aka ayyana su don bai wa kowannen su damar kimtsawa. Da farko dai an tsara gudanar da taron tantancewar ne a ranar Talata a zauren Majalisa wanda daga bisani Fadar shugaban ƙasar ta ɗage zuwa ranar Laraba. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin Majalisar Dattijai, Basheer Lado ya bayyana hakan wa manema labarai. A ranar Larabar da ta gabata ne Shugaba Bola Tinubu ya tsige wasu ministoci biyar tare naɗa wasu goma cikin sahun waɗanda da za a bai wa muƙaman ministoci…
Read More