An shiga murna bayan dawowar wutar lantarki a Kano

Daga BELLO A. BABAJI

Al’ummar yankin Gaida dake ƙaramar hukumar Kumbotso a Jihar Kano, sun shagaltu da murna bayan dawowar wutar lantarki da aka ɗauki tsawon makonni biyu da lalacewarta.

Jihohin Arewacin Nijeriya da dama sun shiga matsalar rashin wuta tun bayan tsaiko da aka samu a tashoshin lantarki na Jihohin Benue da Enugu.

A farkon makon nan ne Kamfanin Raba Wutar lantarki na Ƙasa, TCN ya ce za a kammala aikin gyaran wutar a kwana biyar.

A ranar Laraba ne wutar ta dawo wa jihohi huɗu da suka haɗa da; Filato, Bauchi, Gombe da Benue ƙarƙashin kamfanin raba wuta na Jos.

Mutane a Giada da suka haɗa da mata da yara sun fito don bayyana farin cikinsu kan dawowar wutar da misalin ƙarfe 9 na dare a ranar Laraba.

Kakakin kamfanin raba lantarki na KEDCO dake Kano, Sani Bala Sani ya ce an samu wutar ne daga wani sashi na gaggawa wanda kuma zai bai wa jihar wuta ne na wucin-gadi kafin a kammala ainihin gyaran a mataki na shiyyar baki ɗaya.