Daga USMAN KAROFI
Wata gobara ta lalata turken sabis na sadarwa da ke cikin asibitin Muhammadu Buhari na unguwar Giginyu a birnin Kano.
Kakakin ma’aikatar kashe gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa, “mun sami kira na gaggawa daga wani mai suna Muhammad Garba, wanda ya sanar da ma’aikatar cewa akwai gobara a asibitin Muhammadu Buhari na Giginyu.”
Ya ce, “nan take muka aika ma’aikata daga tashar kashe gobara ta cikin gari zuwa wurin. Da suka isa, suka gano cewa wurin da aka kafa hasumiyar sadarwa mai girman faɗi kamu ashirin da tsayi na ɗaya daga cikin kamfanonin sadarwa a cikin asibiti ne ya kama wuta.”
Kakakin ya ƙara da cewa sakamakon gaggawar da ma’aikatan kashe gobara suka yi, aka yi nasarar kashe gobaran, kuma aka ceto kayayyakin da suka haɗa da batiri na solar, inverter, injinauku masu samar da wutar lantarki da kuma wasu kayayyaki.