Daga RABI’U SANUSI a Kano
Wata kotun Shari’a da ke zamanta a ƙofar Kudu, Jihar Kano, ta aike da Nasiru Mukhtar zuwa gidan yari bisa zargin kai wa limamin masallaci, Malam Murtala Sulaiman, hari yayin sallar asuba a masallacin da ke yankin Tudunwada.
An rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 5 na safe lokacin da ake zargin Mukhtar ya shiga masallacin, ya kai wa limamin hari ta hanyar kama shi a wuya, ya mare shi, sannan ya yayyaga masa kaya tare da karɓar makirifonsa.
Bayan wannan taƙaddama, limamin ya shigar da ƙorafi ga rundunar ‘yan sandan jihar, lamarin da ya kai ga kama Mukhtar.
A lokacin zaman kotun, lauyan da ke kare Mukhtar ya nemi belin wanda ake zargin, yana mai cewa ana buƙatar ƙarin bincike.
Amma alƙali mai shari’a, Malam Isah Rabi’u Gaya, ya bayar da umarnin a yi wa wanda ake zargin gwajin ƙwakwalwa domin a tantance halin lafiyarsa.
Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 22 ga Nuwamba, 2024, yayin da ake ci gaba da tsare wanda ake zargin