Babaji

5712 Posts

Ku biya kuɗin hayar ƙasa ko ku rasa kadarorinku – Wike ga masu filaye a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi kira ga masu filaye a faɗin birnin da su biya duk wani kuɗin ƙa'idar mallakar fili da ake bin su ko kuma su rasa su. Wike ya yi kiran ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da aikin hanyar rukunin bincike ta sojoji da ke Ushafa a ƙaramar hukumar Bwari a ranar Litinin. Minista Wike ya bayyana kuɗaɗen ƙa'idar a matsayin masu muhimmanci ga samar da ababen more rayuwa da ci-gaba wa birnin, don haka ya ce har ya wallafa sunayen waɗanda ake bi bashi a jaridu, ya…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta yi alƙawarin shawo kan matsalar lantarkin Arewa a kwana biyar

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce za a gyara wutar lantarkin da ta lalace a jihohi 17 na Arewacin Nijeriya sakamakon tsaiko da aka samu a tashar lantarki na Shiroro-Kaduna. Ministan Wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya bada tabbacin hakan wa manema labarai jim-kaɗan bayan ganawa da Shugaba Tinubu a Fadar shugaban ƙasa. Ya ce an samu ɗaukewar lantarki ne Arewa sakamakon lalacewa da tashar ta Shiroro-Kaduna ta yi wadda ita ce babbar tashar da ke samar wa yankin wutar lantarki. Adelabu ya ce za a ɗauki tsawon kwanaki uku zuwa biyar ana gyara ta don…
Read More

An kama mutane 34 yayin da aka fara farautar mabarata da ƴan bola a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Aƙalla mutane 34 ne aka kama bayan da hukuma a birnin tarayya Abuja ta ƙaddamar da rufdugu akan mabarata da ƴan bola da makamantansu. Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba su wa'adin tattara komatsansu su fice daga birnin wanda ya ƙare a ranar Lahadi. Cikin waɗanda aka kama akwai mabarata 15 da kuma ƴan bola 19 waɗanda za a miƙa su gidan gyaran tarbiyya da ke Bwari don su karɓi horo. Jami'an da suka gudanar da atisayen sun haɗa da; sojoji, ƴan sanda, DSS, Civil Defence da wasu hukumomin…
Read More

Shubaga Tinubu ya umarci a gaggauta warware matsalar wutar lantarki a Arewa

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna takaicinsa kan baƙin duhun da ya karaɗe Arewacin Najeriya sakamakon rashin wutar lantarki wanda ya haifar da durƙushewar walwala da tattalin arziƙi. Shugaban ya umarci Ministan wutar lantarki da hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta maido da wutar lantarki a duk jihohin Arewa. A wata ganawa da ya yi da Ministan Wutar lantarki, da Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan Harkar Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, Shugaba Tinubu ya bukaci su yi amfani da duk mai yiwuwa wajen ganin an sami wutar tare da umartar Malam Nuhuda ya…
Read More

An naɗa ƴar Shugaba Tinubu Jakadar Hukumar Kula da Almajirai

Daga BELLO A. BABAJI An naɗa ƴar Shugaba Bola Tinubu, Folasade Tinubu-Ojo a matsayin Jakadar Hukumar Kula Almajirai da Ilimin Yaran da ba sa zuwa Makaranta. Babban Sakataren hukumar, Muhammad Sani Idris ya faɗi hakan a yayin wata ziyara da ya kai gidan Tinubu-Ojo da ke Legas. Cikin sanarwar da ya fitar, Sakataren ya ce ƙoƙarin da Tinubu-Ojo ke yi na inganta rayukan al'umma a garuruwa musamman Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta ya taimaka wajen bata muƙamin. Ya kuma yaba wa ƙoƙarinta ga harkokin kasuwanci musamman a ɓangare inganta mata da kiraye-kirayen a tallafa musu. A lokacin…
Read More

Wasu sarakunan gargajiya sun yi tutsu a Sokoto

Daga BELLO A. BABAJI Sama da sarakuna 10 da masu muƙaman gargajiya ne a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato suka yi murabus daga muƙamansu. Kakakin jagororin kuma Ubandoman Sarkin Gobir, Jamil Gobir ya ce sarakunan da mabiyansu sun haɗe kai ne da Sanata Ibrahim kuma Lamiɗon Sakkwato don shawo kan matsalolin rashin tsaro, talauci da koma baya ta fuskar ilmi a gabashin jihar. Ya ce yankin gabashin Sakkwato na buƙatar ɗauki kan tasirin da ta'addanci ya ke yi ga harkokin tattali acikin al'umma. Jami'yyar APC a jihar ta tsage gida biyu sakamakon rikici da ke gudana tsakanin ƴaƴanta,…
Read More

Kotu ta ɗage ƙarar PDP tsagin Mustapha Inuwa zuwa watam gobe a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Babban Kotun Tarayya a Jihar Katsina, ƙarƙashin Mai shari'a Abbas Bawale, ta ɗage ƙarar da PDP ɓangaren Mustapha Inuwa ya shigar wanda ke ƙalubalantar zaɓen shugabannin jam'iyyar da tsagin Sanata Lado Ɗanmarke ya gudanar a jihar. Lauya da ke tsaya wa ɓangaren Lado Ɗanmarke, Mista Isaac Nwachukwu ya ƙalubalanci hurumin kotun na sauraren ƙara da bangaren Mustapha Inuwa ya shigar. Ya ce, duk ƙorafe-ƙorafen su akan zaɓen fidda gwani ne na jam'iyyar ba zaɓen shugabanni wanda harka ce ta jam'iyya. A ɗaya ɓangaren kuma, lauyan su Mustapha Inuwa, Mustapha shiru Mahuta, ya nemi kotun da…
Read More

Za a gurfanar da sojan da ya kashe abokin aikinsa a kotun sojoji

Daga BELLO A. BABAJI Hedikwatar Tsaro, DHQ ta ce wani jami'in sojan ruwa da ke aiki a sansanin jami'an atisayen FANSAN YAMMA a yankin Ɗan-Sadau ya yi ta harbe-harbe wanda a sanadiyyar haka ne ya kashe ɗaya daga cikin abokanan aikinsa. Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Manjo-Janar Edward Buba ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma'a da misalin ƙarfe 3 na yamma a ƙaramar hukumar Ɗan-Sadau dake Jihar Katsina. Ya ce, an kama jami'in mai suna L Seaman Akila A. inda aka karɓe masa bindiga da kuma tsare…
Read More

Daga ƙarshe Fadar Shugaban Ƙasa ta magantu kan Ministar Jinƙai da aka dakatar

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da aka yi wa ministocin shugaban ƙasa garambawul a kwanaki kaɗan da suka gabata, Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya tabbatar da tsige Ministar Jinƙai, Betta Edu daga muƙaminta. Kakakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da gidan talabijin na 'channels', inda ya ce an maye gurbinta ne da wani ɗan Filato. Ya ce, Edu ba ta da gurbi yanzu acikin ministocin Shugaba Tinubu, ya na mai cewa ta yiwa Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta'annati (EFCC) ne ta bada bayanai akan ta da ke tabbatar da rashin…
Read More