Wasu sarakunan gargajiya sun yi tutsu a Sokoto

Daga BELLO A. BABAJI

Sama da sarakuna 10 da masu muƙaman gargajiya ne a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato suka yi murabus daga muƙamansu.

Kakakin jagororin kuma Ubandoman Sarkin Gobir, Jamil Gobir ya ce sarakunan da mabiyansu sun haɗe kai ne da Sanata Ibrahim kuma Lamiɗon Sakkwato don shawo kan matsalolin rashin tsaro, talauci da koma baya ta fuskar ilmi a gabashin jihar.

Ya ce yankin gabashin Sakkwato na buƙatar ɗauki kan tasirin da ta’addanci ya ke yi ga harkokin tattali acikin al’umma.

Jami’yyar APC a jihar ta tsage gida biyu sakamakon rikici da ke gudana tsakanin ƴaƴanta, inda aka samu ɓangaren Sanata Ibrahim Lamiɗo da kuma na tsohon Gwamnan jihar, Aliyu Wamakko wanda kuma shi ne Sanatan Sakkwato ta Arewa.

Tun da aka fara rikicin ne, kusan mambobin APC 40 ne suka ajiye muƙamansu ƙarƙashin Gwamna Aliyu don nuna biyayyansu ga Sanata Lamiɗo.