Gwamnonin Jihohin Arewa 19 sun gana da sarakunan gargajiya a Kaduna a ranar Litinin, don tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafi yankin Arewa. Wannan taron, wanda ya zama wani ɓangare na ƙoƙarin ƙungiyar gwamnonin jihohin arewa don shiga tattaunawa da masu ruwa da tsaki, yana mai da hankali kan matsalolin tsaro, talauci, yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, da sauran ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin.
Wannan ganawar, wadda Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe ya jagoranta kuma Gwamna Uba Sani na Kaduna ya karɓi baƙunci a gidan gwamnatin Kaduna, Sir Kashim Ibrahim House, ta samu halartar gwamnonin jihohin Kaduna, Gombe, Zamfara, Nasarawa, Borno, Bauchi, Kwara da Adamawa. Haka kuma, mataimakan gwamnonin wasu jihohin arewa sun kasance a wurin.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya halarci taron inda ya yiwa gwamnonin bayani kan irin ƙoƙarin da sojoji ke yi don magance matsalolin ‘yan bindiga, ta’addanci da sauran ƙalubalen tsaro da suka addabi yankin Arewa.
Sarakunan gargajiya, ciki har da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar; Shehun Borno, Umar El-Kanemi; Sarkin Zazzau, Nuhu Bamalli; Ohinoyin Ebira, Etsu Nupe Yahaya Abubakar; Sarkin Kazaure da Sarkin Bauchi, duk sun halarci wannan ganawa.
A jawabansu na buɗe taro, Yahaya da Sani sun jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don magance matsalolin tsaro da ke addabar tattalin arzikin arewa, suna mai bayyana cewa lokaci ya yi da za a dauki matakai masu karfi don tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankin.