Za a gurfanar da sojan da ya kashe abokin aikinsa a kotun sojoji

Daga BELLO A. BABAJI

Hedikwatar Tsaro, DHQ ta ce wani jami’in sojan ruwa da ke aiki a sansanin jami’an atisayen FANSAN YAMMA a yankin Ɗan-Sadau ya yi ta harbe-harbe wanda a sanadiyyar haka ne ya kashe ɗaya daga cikin abokanan aikinsa.

Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Manjo-Janar Edward Buba ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 3 na yamma a ƙaramar hukumar Ɗan-Sadau dake Jihar Katsina.

Ya ce, an kama jami’in mai suna L Seaman Akila A. inda aka karɓe masa bindiga da kuma tsare shi, sannan kuma an fara gudanar da bincike game da lamarin.

Janar Buba ya ce bayan kammala binciken ne za a miƙa shi ga kotun sojoji da ke kula da ire-iren batutuwan don ya fuskanci hukunci.

A yanzu dai ana bin hanyoyin da hukumar ta tsara wajen sanar iyalan mamacin halin da ake ciki wanda kawo yanzu ba a bayyana sunansa ba wa jama’a.

Ya kuma yi kira ga gidajen jaridu su kiyaye wajen ruwaito labarin don kar a sanyaya gwiwan iyalan mamacin.