Kwamitin haɗin gwiwa, JAC, na ƙungiyoyin ma’aikatan da ba na koyarwa a jami’o’in, wanda ya haɗa da ƙungiyar ma’aikatan ilimi da haɗin gwiwa, NASU da ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Nijeriya( SSANU) ta umurci mambobinta da su fara taron ƙasa baki ɗaya domin yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Litinin kan rashin biyan albashin watanni huɗu da aka hana.
A cewar shugabannin ƙungiyoyin biyu sun fara yajin aikin ne a daren Lahadi, 27 ga watan Oktoba, 2024.
Ƙungiyoyin dai na neman a biya su albashin watanni huɗu da aka hana su, a ƙara musu alawus alawus da kuma aiwatar da yarjejeniyar da suka ƙulla da gwamnati a shekarar 2009.
Gwamnatin Tarayya ta hanyar Ma’aikatar Ƙwadago ta yi amfani da manufar ‘ba aiki ba albashi’ a lokacin da ƙungiyoyin Ƙwadago huɗu da ke jami’o’i suka tsunduma yajin aiki na tsawon lokaci a shekarar 2022.
Sakataren NASU kuma Comrade Mohammed Ibrahim, Shugaban SSANU, ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a ɗauki matakin ne domin a samu haɗin kai mai inganci da kuma yadda ƙungiyoyin biyu za su kasance da matsaya ɗaya dangane da batun yajin aikin.