Shubaga Tinubu ya umarci a gaggauta warware matsalar wutar lantarki a Arewa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna takaicinsa kan baƙin duhun da ya karaɗe Arewacin Najeriya sakamakon rashin wutar lantarki wanda ya haifar da durƙushewar walwala da tattalin arziƙi.

Shugaban ya umarci Ministan wutar lantarki da hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta maido da wutar lantarki a duk jihohin Arewa.

A wata ganawa da ya yi da Ministan Wutar lantarki, da Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan Harkar Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, Shugaba Tinubu ya bukaci su yi amfani da duk mai yiwuwa wajen ganin an sami wutar tare da umartar Malam Nuhu
da ya tura isassun jami’an tsaro da kayan aiki ciki har da jiragen sama don su kare injiniyoyin da ke gyara injikan wuta na Shiroro.

Shugaban ya yi gargaɗin cewa gwamnati ba za ta sake lamuntar yin zagon-ƙasa ga kayayyakin amfanin jama’a da gangan ba.

Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da jami’an tsaro da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen kare kadarorin al’umma.

By Babaji