Boko Haram sun kashe sojoji 40 a wani sabon hari a Chad

Aƙalla sojojin Chadi 40 ne suka mutu sakamakon wani sabon hari da Boko Haram suka kai a kusa da kan iyakar Nijeriya, wanda ya haifar da wani farmakin sojojin ƙasar domin kamo mayaƙan.

‘Yan Boko Haram sun kai hari kan wani sansani da ke ɗauke da fiye da sojojin Chadi 200 a yammacin Lahadi, a yankin Tafkin Chadi, wurin da ya sha fama da hare-hare daga ƙungiyoyin ‘yan bindiga daban-daban, kamar yadda majiyoyi na gida suka bayyana wa AFP.

Fadar shugaban ƙasar Chadi, ta bayyana cewa harin ya auku ne a kusa da garin Ngouboua da ke yammacin ƙasar, “inda ya bar aƙalla mutane 40 sun mutu.” Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby Itno ya ziyarci wurin da safiyar Litinin, inda ya ƙaddamar da wani farmakin ɗaukar fansa “don bin sawun masu kai harin da farautar su zuwa mafakar su mafi zurfi,” in ji sanarwar.

Kuma, babban kwamandan rundunar sansanin ya shiga cikin waɗanda aka kashe, kamar yadda wani jami’i ya bayyana kan sharaɗin a sakaya sunansa. Ma’aikatan sojin sun bayyana cewa “Boko Haram sun ƙwace makamai da kayan aiki kafin su tsere.”

Sojojin sun ce Boko Haram sun kama sansanin, sun ƙwace makamai, sun ƙona motocin yaƙi, sannan suka bar wurin.

Kakakin rundunar sojojin yankin, Janar Saleh Haggar Tidjani, ya tabbatar wa AFP cewa duk da mummunan asarar da aka samu, “Sojojin mu sun mamaye wurin kuma suna ci gaba da farautar yan ta’addan.”

Shugaban Chadi ya bayyana cewa yana nan akan matsayinsa na kare ƙasar da kuma tabbatar da tsaron yankin, yana tabbatar wa al’ummar ƙasar da cewa za a ɗauki matakan kare lafiya da tsaron ƙasar daga hare-haren.