10
Jun
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa tsohon mataimakin sufetan ƴan sanda na ƙasa, Hashimu Argungu a matsayin sabon shugaban hukumar kula da harkokin ƴan sanda ta PSC. Argungu ya maye gurbin Solomon Arase ne da shugaba Tinubu ya tsige, wanda ke shugabantar hukumar tun watan Janairun 2023, a lokacin gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari. Sanarwar ta fito ne daga ofishin mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale a ranar Litinin. Haka nan, sanarwar ta ce Tinubu ya naɗa Chief Onyemuche Nnamani a matsayin sakataren hukumar da kuma Taiwo Lakanu mai ritaya a…
