Ayarin motocin Gwamnan Katsina sun yi hatsari

Daga UMAR GARBA a Katsina

Tawagar motocin Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ta yi hatsari a daren jiya juma’a

Hatsarin ya faru ne a kusa da ƙauyen Jiqamshi lokacin da Gwamnan da kuma tawagar motocinsa ke kan hanyar zuwa Ƙaramar Hukumar Ƙafur mahaifar shi inda zai kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar jiha ranar Asabar.

Rahotannin sun ce jami’an tsaro biyu da ke tare da tawagar, Kabir Adamu da Nura Safiyanu, suka rasa rayukansu a yayin da wasu suka jikkata.