Ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba na barazana ga madatsar ruwan Liberty a Jos – Jami’i

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Manajan Darakta na Kamfanin Samar da Ruwan Sha na Jos, Mista Apollos Samchi, ya bayyana cewa ci gaba da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a kusa da katangar madatsar ruwan Liberty da ke Jos, na barazana ga inganci da amincin wannan muhimmin wurin tara ruwa.

Samchi ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Jos ranar Litinin, inda ya ce masu haƙar ma’adinan sun ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da gargaɗin da aka yi musu, ba tare da la’akari da illar da hakan ka iya haifarwa ga ƙarfin katangar madatsar ruwan da kuma tsaron al’ummomin da ke kewaye da ita ba. Ya bayyana cewa, madatsar ruwan Liberty ce ke samar da ɗanyen ruwa ga masana’antar tace ruwan Laminga, don haka kare ta na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da ɗorewar samar da ruwan sha a birnin Jos da yankunan da ke kewaye da shi.

Manajan daraktan ya yi gargaɗin cewa ci gaba da haƙar ma’adinai a kusa da katangar madatsar ruwan na iya ƙara raunana ta, tare da jefa al’ummomin da ke maƙwabtaka da wurin cikin haɗari.

Ya yi kira ga masu gudanar da haƙar ma’adinan ba bisa ƙa’ida ba da su gaggauta dakatar da ayyukansu, yana mai bayyana hakan a matsayin babbar barazana ga rayukan jama’a da kuma muhimman ababen more rayuwa da suka shafi samar da ruwa. Samchi ya ce Gwamnatin Jihar Filato na sane da halin da ake ciki, kuma za a ɗauki tsauraran matakai domin dakatar da waɗannan ayyuka da kuma kare madatsar ruwan.

Ya jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa domin kare madatsar ruwan da kuma kauce wa aukuwar wani bala’i, yana mai cewa ci gaba da gudanar da aikinta na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ruwan sha ga babban birnin jihar.

By ukarofi