Ayyukan raya jiha: Gwamnan Jihar Yobe, Mala Buni ya ciri tuta – Hon. Dala Buni

Daga GAMBO ISA

Shugaban ƙaramar Hukumar Gujba a Jihar Yobe, Honorabul Alhaji Dala Mala Buni ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni bisa ayyukan raya ƙasa a jihar.

Dala ya bayyana haka ne a cikin makon nan yayin wata tattaunawa da wakilinmu a Abuja, inda ya zayyana wasu daga nasarorin da gwamnan ya samu a fannin jin daɗi da walwalar al’umma ta fuskar kayayyakin more rayuwa, noma, ilimi, kiwon lafiya, gina manyan kasuwanni na zamani da sauransu.

Honorabul Dala Buni ya lissafo nasarorin da suka haɗa da, shirye-shiryen da suka shafi al’ummar jihar kaitsaye, kamar gina manyan kasuwannin zamani a ƙananan hukumomi 17 ciki har da Damaturu babban birnin jihar, Nguru, Bade, Potiskum da Gaidam.

Honorabul Alhaji Dala Mala Buni ya yaba da aikin gine-gine tare da gina babbar kasuwar zamani a gundumomin da ke cikin garin Gujba.

Honorabul Dala, ya yaba da yadda gwamnan ke yaƙi da ‘yan ta’adda, inda Gwamna Buni yake taimaka wa  jami’an tsaron CJTF domin yaƙar ‘yan ta’addar Boko Haram a jihar.

Kazalika ya ce gwamnan ya yi tasiri ga rayukan marasa galihu a cikin Gujba da sauran ƙananan hukumomin jihar inda ya buƙace su da su tallafa wa yawancin shirye-shiryensa.

Honorabul Dala ya jinjina wa Gwamna Mai Mala Buni ta fuskar haɓaka ilimi, horas da likitoci, malaman aikin jinya da ungozoma da gina makarantu a cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da wuraren ba da magani a gundumomi, a cikin ƙananan hukumomi 17, don ingantaccen tsarin kiwon lafiya.

Honorabul Dala ya buƙaci al’ummar ƙaramar hukumar Gujba da su shiga cikin shirin noma da shirin gwamna inda gwamnati ta samar da kayan amfanin gona don bunƙasa noma.

Honorabul Dala ya shawarci matasa da su kasance jakadan yankin a kodayaushe.

Ya buƙaci matasa da su yi biyayya ga dokokin tsarin mulki da dokokin ƙasa, su guji shan miyagun ƙwayoyi, su riƙa saurare da mutunta dattijai a cikin al’ummarsu ko yankin da ke sana’ar kasuwanci da koyar da sana’o’i domin dogaro da kai.

Haka kuma ya shawarci dattawan yankin da su tallafa wa shirye-shiryen gwamnati wajen gina ƙaramar hukumar.

Ya ce salon jagoranci na gwamna Honorabul Mai Mala Buni na tare da kafa harsashin da ministan harkokin ‘yan sanda na yanzu Sanata Ibrahim Gaidam ya kafa.

Ya shawarci takwarorinsa shugaban ƙananan hukumomi 17 da su fara gudanar da shirye-shiryen Gwamna Mai Mala Buni da su kasance masu riƙon amana ga jama’arsu, domin suna sa ran za a kai musu ribar dimokuraɗiyya.

Honorabul Dala ya shawarci matasa, dattijai a cikin al’umma, Gujba musamman da su yi wa ƙasa addu’a, ya kuma jajanta wa al’ummar jihar Borno, gwamnan zartarwa Farfesa Baba gana Zulum da Shehun Borno kan bala’in ambaliyar ruwa ya buƙaci a yi musu addu’a. attajirai da ke ba da agaji don ba da gudummawa ga wadanda ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a ƙarshen shekarar da ta gabata.

Ya yaba wa gwamnan bisa samar da sufurin zamani zuwa layin Yobe domin tallafawa rage raɗaɗin talauci.

Kazalika ya yaba da salon jagorancin Sarkin Gujba da Sarkin Gudi, da shugabancin babbar jam’iyyar APC ta ƙasa ƙarƙashin Dr Abdullahi Ganduja APC da shugaban jam’iyyar na jihar Yobe Honorabul Muhammad Gadaka.