Azumin bana: Ga talauci ga tsadar kayan masarufi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Watan Ramadan dai shi ne wata na tara a lissafin watannin Musulunci kuma yana daga cikin watanni masu alfarma. Hasali ma a cikinsa ne aka saukar da Alƙur’ani mai girma, wanda ya ƙunshi dukkan hukunce-hukuncen addinin Islama.

Shi dai azumi shi ne kamewa daga cin abinci ko sha da kuma jima’i, haka kuma ana son mai azumi ya ƙara kamewa daga barin duk wani zance na alfasha ko kuma aikata zunubi.

A na daina cin abinci ko sha ne tun daga fitowar alfijir har faɗuwar rana. Wannan ya sanya yawaitar buƙatuwa da abin kai wa baka a lokacin buɗe-baki. Hakan ya na haifar da hauhawar saye da sayarwa, musamman na ababen ci da sha ɗin, wanda hakan ke iya haifar da tsadarsu.

Sai dai kuma a bana, a na ganin cewa, lamarin ya na nema ya wuce gona da iri na tsadar farashin kaya, baya ga tsananin talauci da ya addabi alu’ummar Musulmi.

Alhaji Nasiru Nasco Ɗakingari, wanda mazaunin Jihar Kebbi ne, ya bayyana cewa, ba shakka mutane su na cikin talauci, sannan kuma ga abinci yana tsadar gaske, wanda ya sanya dole magidanta sauya ƙudurorinsu na hidimar iyali, saboda idan ana neman abinci ba zancen kayan alatu ake yi ba.

A baya kowa ya sani, idan watan Ramadan ya zo, za ka ga gwamnatin jiha ko ta tarayya ko ma ƙananan hukumomi su na raba abinci da kayan alatu da kuma kuɗi, amma yanzu tuni an daina a mafi yawan gurare, duk da cewa, wannan yana ɗan taimakawa wajen rage waɗansu matsaloli. 

Wani magidanci a Kebbi mai suna Malam Garba Dandare GG ya bayyana damuwarsa bisa ga irin yadda ‘yan kasuwa ke tsauwalawa musamman a irin wannan lokacin da ya kamata su sassauta wajen harkokin kasuwancinsu, domin samun rahama.

A baya ana sayar da kwalbar manja Naira 700, amma yanzu ta kai Naira 1,050, mudun sukari daga Naira 800 ya haura zuwa Naira 1,000,  madarar gwangwani ta ruwa daga Naira 170, ta koma Naira 300.

Haka zalika, a ɓangaren kayan marmari, ƙwayar lemo ɗaya ya soma daga farashin Naira 50, yayin da kankana ƙarama ce za ka iya samu a kan Naira 500, yayin da mudun gero ya tashi daga Naira 300 zuwa 400.

Sannan ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su ji tsoron Allah wajen harkokin kasuwancinsu, musamman a cikin wannan watan mai alfarma.

Alhaji Ibrahim Danjimma (Imani) wani ɗan kasuwa ne da ya bayyana wa wakilin Blueprint Manhaja cewa, dalilan da ke sanya kayan masarufi tsada suna da yawa. Amma dai na farko, akwai hauhawar farashin Dala da kuma Saifa da ya ke a Nijeriya. Su ne mafi yawan ’yan kasuwa ke ma’amala da su ta hanyar cinikayya. 

Dalili na biyu kuma, kowace shekara manyan ‘yan kasuwa suna sayen kayan alatu, su adana, don jiran irin wannan lokacin na azumi, domin cin ƙazamar riba. Haka zalika, yawaitar buqata tana bayar da gudunmawa wajen ƙara tsadar kaya a irin wannan lokacin.

Ibrahim Imani ya ƙara da cewa, wannan ba wata mafita da ta wuce kowa ya ji tsoron Allah ya gyara. Gurin da ya san ba a daidai ya ke ba saboda su da kansu talakawa suna da ta su matsala musamman a irin wannan lokacin ne magidanci zai samu kyautar abinci maimakon ya kai gidansa, don amfanin iyali, amma sai dai kawai ya kai kasuwa ya sayar, don wata buƙatarsa ta ƙashin kansa.

Ko ma dai mene ne, a yanzu dai talakawan Nijeriya su na fama da hannu-baka-hannu-ƙwarya ne, don samun abin salati, saboda baya ga tashin gwauron zabo da farashin abinci ya yi, kuɗin shiga kuma ya na yi wa talaka wahalar samu. Idan ma ya samu, faɗuwar darajar Naira ya sanya kuɗin ba ya yi wa Malam Talaka gwaɓi.