Lambar NIN: Waɗanda aka rufe layukansu su yi tururuwa ofisoshin kamfanonin sadarwa

Daga AMINA YUSUF ALI

Wasu masu amfani da layukan sadarwa sun shiga tsaka mai wuya a ranar Larabar da ta gabata bayan da suka wayi gari kamfanonin sadarwa suka rufe musu layukan waya. Wato aka hana su kiran waya gabaɗaya. Hakan ya biyo bayan umarnin gwamnatin Tarayya na a rufe layin dukkan wanda bai yi rajistar  shaidar ɗan ƙasa (NIN) a layin nasa ba.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Gwamnatin Tarayya ta ba da umarni ga dukkan kamfanonin sadarwa da su tilasta wa ‘yan Nijeriya yin katin shaidar ɗan ƙasa da kuma yin rajistar wayarsu da lambar ɗan ƙasa. Ta nemi kamfanonin da su rufe dukka layukan wayar mutanen da suka bijirewa rajistar layukan nasu har i zuwa ranar da da aka ce ita ce ranar ƙarshe da aka ba da damar yin rajistar. Wato zuwa ranar 31 ga watan Maris ɗin shekarar nan.

A yayin da take ba da umarnin rufe layukan marasa rajistar, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, a yanzu haka kwastomomi miliyan 125 ne suka ajje layukansu don yin rajistar NIN ɗin. 

Hukumar kula da sadarwa ta Nijeriya kuma ta bayyana cewa, zuwa ƙarshen watan Fabrairun 2022 Nijeriya tana da mutane miliyan 197.77 da suke amfani da layukan sadarwa.

Hakan ya nuna kenan, wannan dokar rufe layukan sadarwar za ta shafi kwastomomi miliyan 72.77masu amfani da layukan sadarwa a Nijeriya.

Bayan da ƙungiyar shugabannin kamfanonin sadarwa masu lasisi ta Nijeriya (ALTON) suka ba wa gwamnati tabbacin cewa za su yi biyayya a kan umarnin da ta ba su na rufe layuka marasa rajistar NIN. Kamar yadda suka bayyana a ranar litinin ɗin da ta gabata. 

A ranar Talata ne kuma dubban mutane suka wayi gari da layukansu sun kasa kiran waya. Kuma rahotanni masu tushe sun bayyana cewa, waɗanda aka rufe wa layukan sun yi ta dafifi i zuwa cibiyoyin kamfanonolin sadarwar domin yin rajistar NIN a layukansu.