Ba a sauya wa tuwo suna

Spread the love

Daga IBRAHIM YAYA

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Ƙasar Sin, ita ce kaɗai halastacciyar gwamnati dake wakiltar ƙasar Sin. Haka kuma kasancewar ƙasar Sin ɗaya tilo a duniya, ita ce babbar manufar da ƙasashen duniya suka amince da ita, kana tushen siyasa na raya hulɗa tsakanin Sin da duƙ ƙasashen da suka ƙulla ko ma suke son ƙulla alaƙa da ƙasar Sin.

Yanzu haka akwai ƙasashe 180 a duniya, waɗanda suka amince tare da goyon bayan manufar ƙasar Sin ɗaya tilo a duniya, kuma wannan ita ce yarjejeniya ta zahiri da ƙasashen duniya suka amince da ita.

Ƙasar Amurka na daga cikin ƙasashen da suka amince da wannan manufa, baya ga sanarwoyi uku da ƙasashen biyu suka aminta da su a kan alaƙar dake tsakaninsu, amma har yanzu Amurka ta yi biris tare da neman lalata tushen siyasa na hulɗar dake tsakaninta da ƙasar Sin, inda take ci gaba da hulda da yankin Taiwan na ƙasar Sin.

Sanin kowa ne cewa, Taiwan ba ƙasa ba ce, wani ɓangare ne na ƙasar Sin. Duk abun da ’yan aware suke yi na jirkita gaskiya, ko kaɗan ba zai taba canja gaskiyar lamarin ba, wato babban yanki da kuma yankin Taiwan duka suna ƙarƙashin ikon Jamhuriyar Jama’ar ƙasar Sin ne.

A baya-bayan ne, wasu ’yan majalisun dokokin Amurkar suka ziyarci yankin, abin da masu fashin baƙi suka bayyana a matsayin wani salo na taƙala da gangan, da take ƙa’idar kasancewar ƙasar Sin ɗaya tak a duniya da kuma tanadin sanarwoyin haɗin gwiwa guda 3 da Sin da Amurka suka fitar. Ziyarar da ɓangaren na Sin ya yi Allah wadai da ita.

Masu fashin baƙi na cewa, ziyarar jami’an na Amurka munafurci ne da nuna rashin gaskiya, domin a baya Amurka ta ce ba ta goyon bayan ’yancin kan Taiwan, a daya ɓangaren kuma, tana aikewa da wani mummunan sako ga masu rajin ɓallewa. Kuma ƙasar Sin tana adawa da hakan.

A ƙoƙarin da ƙasar Sin ke yi na kara fahimtar da ƙasashen duniya game da manufar ƙasar Sin daya tak a duniya, sanarwar da aka fitar bayan kammala cikakken zaman karo na shida na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19, ta bayyana ƙarara cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba ƙa’idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kuma matsaya irin wannan da aka cimma a shekarar 1992, wadda ke adawa da ayyukan ’yan aware dake neman ’yancin kai na Taiwan, da tsoma baki daga waje.

Wannan ya ƙara fayyace tsayin daka na ƙasar Sin, da kuma matsayinta na kare ikon mallakar ƙasa da cikakken yankunanta, har ma da tsaro da moriyar ci gabanta baki ɗaya. Ta kuma sha alwashin daƙile duk p kutse daga waje da masu neman ’yancin kan Taiwan. Kuma duk wanda bai ji gari ba, to zai ji Hoho.

Ƙasar Sin na kara jaddada cewa, duk ƙasar dake son kulla hulɗar diflomasiya da ƙasar Sin, waijibi ne ta martaba wannan manufa. Wato Ƙasar Sin daya ce tak a duniya, Ma’ana ita ce Ba a Sauyawa Tuwo Suna.

By Editor