An kammala bikin ranar Sinanci ta MDD ta 2022 da taron CMG na biyu na nuna bidiyon da aka naɗa a ƙetare cikin nasara

Daga CMG HAUSA

A yau Laraba ne aka kammala bikin ranar Sinanci ta MDD ta shekarar 2022, da taron kafar talabijin da radio ta ƙasar Sin CMG na biyu, na nuna bidiyon da aka naɗa a ƙetare cikin nasara.

An gudanar da bukukuwa ne a birnin Geneva. Kuma babbar daraktar ofishin MDD dake Geneva Tatiana Varovaya, da shugaba, kuma babban editan kafar CMG Shen Haixiong, da wakilin dindindin na ƙasar Sin a ofishin MDD, da sauran hukumomin ƙasa da ƙasa dake Switzerland jakada Chen Xu, sun halarci bikin ta yanar gizo.

Mai fassarawa: Saminu daga CMG Hausa