Sharhi: Bikin Easter da ke cike da harbe-harben bindiga

Daga CMG HAUSA

A ƙarshen makon da ya gabata, munanan harbe-harben bindiga da aka samu a sassan ƙasar Amurka, sun hallaka mutane tare da jikkata wasu da dama, waɗanda suka girgiza al’ummar ƙasar da ke bikin Easter.

A birnin Pittsburgh na jihar Pennsylvania, harbe-harben bindiga sun hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu a ƙalla 8. A Hampton, South Carolina, wasu mutane 9 sun ji raunuka sakamakon harbe-harben bindiga, a yayin da a birnin Columbia, babban birnin jihar, harbe-harben bindiga da aka yi a wani kanti ya jikkata wasu mutane 14. Sai kuma a birnin Syracuse na jihar New York, harbe-harben bindiga da aka yi sun yi sanadiyyar mutuwar mutum guda, tare da ji wa wasu 4 raunuka.

Alƙaluman da aka samar sun yi nuni da cewa, daga farkon bana zuwa ranar 17 ga wata, mutane 12,502 sun rasa rayukansu a sakamakon harbe-harben bindiga a ƙasar Amurka, a yayin da wasu 10,024 suka ji raunuka.

Shin ba ƙasar Amurka ce ke daukar kanta a matsayin abin koyi wajen kare haƙƙin bil Adam ba? Me ya hana gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakai na shawo kan matsalolin harbe-harben bindiga a ƙasar? Me ya sa ake matuƙar shan wahala wajen aikin ƙayyade mallakar bindigogi a ƙasar?

Mai zane:Mustapha Bulama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *