Ba daidai ba ne bai wa jami’an FRSC bindigogi – Mai sharhi kan tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani mai sharhi akan harkar tsaro kuma shugaban ƙungiyar matasan Arewa masu son zaman lafiya da tsaro, mai suna Kwamared Salihu Mahmud, ya ƙi goyon bayan ƙudirin Majalisar Wakilai da ke neman a bai wa wasu jami’an hukumar kiyaye haɗura (FRSC) bindigu.

Ya bayyana hakan a matsayin abu wanda ya ci karo da tsarin gudanar da tituna a mataki na duniya.

Kwamared Mahmud ya yi kira ga ƴan majalisa su yi watsi da buƙatar hakan, ya na mai cewa akwai jami’an ƴan sanda na kan hanya da ke aiki tun kafin a ƙirƙiri FRSC waɗanda har zuwa yanzu ba a ba su damar riƙe makamai ba.

Ya ce, asalin abin da ya sa aka samar da FRSC shine don a samu raguwar aukuwar haɗura a titinan Nijeriya.

By Babaji