
Daga BELLO A. BABAJI
Wasu ƴan bindiga sun tare babbar hanyar Funtua zuwa Gusau inda suka yi garkuwa da matafiya da dama.
Ƴan bindigar sun tare hanyar ne a yankin ƙauyukan Kucheri da Magazu na ƙaramar hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara.
Kakakin ƴan sandan jihar ASP Yazid Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce kawo yanzu ba a san adadin wanɗanda aka yi garkuwa da su ba.
Ya ce hukumomin tsaro sun haɗe kai wajen ganin an ceto su daga hannun ƴan ta’addar.
A ƴan kwanakin nan dai ƴan bindiga sun sha kai hare-hare a jihohin Katsina da Zamfara inda su ke kashewa tare da yin garkuwa da mutane duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi na kawo ƙarshen ta’addanci a shiyyar Arewa-maso-Gabas da ma Nijeriya gaba ɗaya.
