Rashin tsaro: Kwamandan jami’an CPG na Zamfara ya tsallake rijiya da baya

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Babban kwamandan rundunar kare al’umma ta CPG reshen Jihar Zamfara, Burgediya Janar Lawal B. Muhammad (rtd) ya tsallake riya da baya daga harin gungun ƴan bindiga a lokacin da suka buɗe wa motarsa ​​wuta a kan babbar hanyar Funtua-Gusau.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Asabar a ƙauyen Kucheri da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar.

A cewar majiyarmu wanda ya nemi a sakaya sunansa yayin ganawa da manema labarai, Kwamandan yana kan hanyarsa ta dawowa Gusau daga Kaduna inda isarsa ƙauyen ke da wuya sai ya gamu da ƴan bindigar.

Kwamandan ya samu mummunan harbin bindiga a ƙafarsa ta hagu, sannan harsashin ya shafi ɗaya gefen kafarsa ta dama.

Majiyar ta ci gaba da cewa, an ɓarnata was motoci da sakamakon harbe-harben bindiga da ƴan ta’addan suka yi, inda kuma wasu fasinjoji sun jikkata a yayin farmakin.

Ta ƙara da cewa, lokacin da aka sanar da dakarun sojojin Nijeriya game da lamarin, sun mayar da martani nan take tare da fatattakar ƴan bindigar.

Wani shaidar ya bayyana wa wakilinmu ƙarin haske game da lamarin inda ya ce wasu fasinjojin sun jikkata yayin da ƴan bindigar suka yi awon gaba da wasu matafiya a yayin samamen.

Ya ce, babu wani sojan da ya samu rauni, amma motar da sojojin ke aiki da ita ta lalace sakamakon harbe-harben bindigogi da dama.

Blueprint ta ruwaito cewa, gwamnan jihar, Dauda Lawal, ya kai ziyara a asibitin da aka kwantar da kwamandan inda ya jajenta masa kan al’amarin.

A kwanakin baya ne ƴan bindigar suka kashe jami’an tsaro na CPC guda tara a jihar, a wani harin kwantan-ɓauna da suka kai a babban shingen binciken jami’an CPG da ke hanyar Gusau-Funtua a Tsafe, inda suka yi awon gaba da makaman su.

By Babaji