
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Barau I. Jibrin ya roƙi masu shirya zanga-zangar gama-gari su sake yin nazari kan hukuncinsu tare da janye wa daga batun, don kar a yamutsa sauran zaman lafiyar da ya rage wa Nijeriya.
Barau, wanda shi ne Mataimankin Kakakin Majalisar ECOWAS na farko, ya ce Tinubu na muhimmin ƙoƙari wajen ganin an magance matsalolin Nijeriya.
Wata takarda da ta fito daga ofishin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ta ce Barau ya yi kira ga masu hura wutar zanga-zangar kan cewa su bai wa Shugaba Tinubu ƙarin lokaci don ƙaddamar da muhimman abubuwa da tsare-tsaren gwamnatin kamar yadda ya ke a jadawalin sabonta ayyukan cigaba ga tattalin arziƙin Nijeriya.
Ya ce, tun ranar da aka rantsar da gwamnatin a shekarar 2023 ta ke aiki tuƙuru domin dawo da martabar ƙasar ta cigaba don al’ummar ƙasa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa, rattaɓa hannu kan ƙudurin hukumomin raya yankunan Arewa-maso-Yamma da Kudu-maso-Gabas cikin dokar ƙasa da Tinubu ya yi na ɗaya daga cikin matakan da ya ɗauka wajen shawo kan matsalolin da su ka shafi dukkan ɓangarorin ƙasar.
Kazalika, ya nusar da masu shirya zanga-zangar, ya na mai bada misali da irin yadda aka yi a ƙasashen Siriya, Yemen, Libya da Sudan, inda ya ce daga ta lumana aka fara waɗanda daga baya su ka zama sabuban zubar da jini inda su ka haifar da koma baya wa ƙasashen.
“Wannan ƙasarmu ce; ba mu da wajen zuwa da ya wuce Nijeriya da iyaye da kakanni su ka gadar mana. Ku yi haƙuri kuma ku ƙara lokaci. Za mu dawo da ita dai-dai. Ƙoƙarin da sabuwar gwamnatin ke yi zai bada sakamakon da ake buƙata da yardar Ubangiji”, inji shi.
