Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba sai an samu canji a siyasar Arewa – Hon. Haruna Yahaya

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Tsohon ɗan takarar majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar Hukumar Rogo a ƙarƙashin Jam’iyyar ADC Hon Haruna Yahaya Kadana ya bayyana cewa samun kwanciyar hankalinsa a yanzu ba zai abinda bai wuce al’umma su samun shuwagabanni nagari ba.

Hon Kadana ya bayyana haka ne a wata zantawa da manema labarai yayin da yake tsaka da murnar ƙara shekarunsa da ya samu a duniya da Allah ya azurta shi da su da ya gudana a Cocin Angilican dake ƙaramar Hukumar Fagge.

Matashin ɗan siyasar ya kuma soki batun sayar da fom ɗin takara akan Naira milyan 10 na matakin zaɓen ƙaramar hukuma, yayin da kuma ya bayyana shi ma na Kansila bai kamata ya kai naira milyan 5 ba.

“Wannan zai iya kawo koma baya ga nagartattun ‘yan takara suka sa samun damar sayen wannan fom, ka ga har yanzu daga su sai ‘ya’yansu kenan.

Kadana ya kuma bayyana wannan tsarin sayar da fom a matsayin ganin batun cin hanci da rashawa da ake buƙatar daƙilewa a matakin ƙasa har zuwa ƙananan hukumomi a Nijeriya ba zai taɓa gushewa ba.

Ya kuma buƙaci cewa idan mulki mai girma Gwamna Abba Kabir da ya sa baki domin a sauƙaƙa wa masu buƙatar takara su samu sauƙin sayen wannan takaradar takara don yi wa al’umma aiki.

“A nan ma muna kira ga Hukumar Zaɓe ta jihar Kano da ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin waɗanda suka kamata ne ta sayar ma da wannan fom tare da nemo hanyar da za su samu sauƙin sayen wannan fom.

Hon. Haruna Yahaya ya kuma ci gaba da bayyana cewa babu yadda za a yi ɗan takara ya sayi fom da tsada amma a yi tunanin ya yi wa jama’a aiki, wannan bakowa zai amince da hakan ba.

“A yanzu muna tunanin yadda al’umma za su samu sauƙin rayuwa ne ba wai wani batun sauya sheƙa ko jam’iyya ba.”

A yayin taron ne dai jama’a masoya daban-daban suka taya Hon. Haruna Yahaya Kadana murna zagayowar haihuwar ta shi tare da yi masa fatan alkhairi a dukka abinda ya sa gaba, musamman yadda yake kulawa da al’umma tun daga matakin ƙaramar hukumar shi ta Rogo har zuwa zagayen arewacin ƙasar nan dama wani yanki na Kudu.

By ukarofi