Luis Suarez ya sanar da yin ritaya daga buga wa tawagar Uruguay ƙwallon ƙafa.
Mai shekara 37 ya ɓarke da kuka a lokacin da ya ce wasan da ƙasar za ta kara da Paraguay a neman shiga kofin duniya ranar Asabar, shi ne na ƙarshe da zai yi.
Tsohon ɗan wasan Liɓerpool da Barcelona shi ne kan gaba a yawan ci wa kasar ƙwallaye mai 69 a raga a karawa 142 – ya fara taka mata leda a Fabrairun 2007 a karawa da Colombia.
Suarez ya buga wa Uruguay manyan gasa tara a faɗin duniya.
An yi masa jan kati a gasar cin kofin duniya a 2010, bayan da ya taɓa ƙwallo da hannu a kan layin raga a wasan da ya hana Ghana kai wa zagayen daf da ƙarshe.
Asamoah Gyan ya ɓarar da fenariti, inda Uruguay ta kai zagayen daf da ƙarshe a karon farko tun bayan shekara 40.
A 2011, Suarez ya ja ragamar Uruguay ta lashe Copa America a Argentina, shi ne na biyu a yawan cin ƙwallaye a gasar mai huɗu a raga.
A shekarar 2014 a gasar kofin duniya ya ci ƙwallo biyu, inda Uruguay ta doke Ingila a karawar cikin rukuni, amma bai buga wasan zagaye na biyu ba sakamakon da aka dakatar da shi wasa huɗu, bayan da ya ciji Giorgio Chiellini a wasan ƙarshe a cikin rukuni da Italiya.
An dakatar da Suarez wasa tara, hakan ya hana shi buga wa Uruguay Copa America a 2015.
Suarez ya buga gasar kofin duniya a 2018 da 2022 da halartar gasar Copa America biyar.
